Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Dauda Lawal Ya Ƙaddamar Da Manyan Ayyuka A Bukkuyum

Gwamna Dauda Lawal ya kaddamar da aikin gina titi tare da sake gina babbar asibitin karamar hukumar Bukkuyum. Gwamnan ya ziyarci karamar huk...

Gwamna Dauda Lawal ya kaddamar da aikin gina titi tare da sake gina babbar asibitin karamar hukumar Bukkuyum.

Gwamnan ya ziyarci karamar hukumar Bukkuyum a yau Talata don raba muhimman kayan anfanin gona ga manoma don rage  radadin da annobar korona ta haifar da farfadowa da tattalin arziki karkashin kulawar FADAMA III.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce aikin titin da za a fara daga mahadar Mallawama zai kai kilomita 19.2 a karamar hukumar Bukkuyum.

Ya kara da cewa za'a gudanar da gyare-gyare sosai a babbar asibitin Nasarawar Burkullu domin inganta harkokin kiwon lafiya.

A jawabin da ya gabatar a wajen kaddamar da aikin, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa aikin titin mai tsawon kilomita 19.2 zai shafi hanyar Mallamawa-Zarummai-Bukkuyum da Bukkuyum-Birnin Zauma-Gummi.

“A madadin gwamnatin jihar, ina mai farin cikin kaddamar da wannan aikin hanyar. Wannan aiki yana cikin alkawuran da muka yi wa al’ummar Zamfara a lokacin yakin neman zabe, kuma Alhamdulillahi muna kan cikasu.

“Burinmu shi ne mu kawo wa al’ummar Zamfara duk wani romon mulkin dimokuradiyya, kuma wannan aiki farawa ne  daga cikin tsare-tsaren da muke dasu na inganta rayuwar al'umma.

“Mun riga mun ba ’yan kwangila umarnin fara wannan aiki, kuma muna da yakinin cewa aikin zai haifar da gagarumin sauyi ga mutanen Bukkuyum.

"Ina kira ga kowa da kowa da ya bai wa 'yan kwangilar hadin kai don gudanar da ayyukansu."

A yayin kaddamar da rabon kayayyakin noma a karamar hukumar ta Bukkuyum, Gwamna Dauda Lawal ya yi kira ga wadanda zasu ci gajiyar wayannan kayan amfanin gona da su yi amfani da damar da suka samu wajen inganta noman su da kuma inganta rayuwarsu.

“Wannan yunkuri namu  yana tabbatar da kokarinmu na dakile illar cutar ta annobar korona ta haifar.

“Ta hanyar zagayen wasu daga cikin kananan hukumomin dake fadin yankunan mazabu uku (3) na jihar, muna  kara wayar da kan jama’a  ta hanyar karfafa gwiwar wadanda suka amfana da shirin da su yi amfani da shi ta hanyar da ta dace.

“Wannan tsari ya mayar da hankali ne a kan aikin gona, lura da muhimmiyar rawar da yake takawa a tattalin arzikin jihar, wanda galibin sa noma ne. Sama da kashi 80% na adadin jama'ar Zamfara manoma ne. A karkashin wannan shirin, sama da manoma 100,000 a fadin kananan hukumomin (14) za'a karfafa musu kayan aikin noma da iri a cikin shekaru hudu masu zuwa na gwamnatin mu."

Da yake kaddamar da aikin gyara da inganta babbar asibitin Nasarawar Burkullu, Gwamna Lawal ya jaddada cewa za'a samar da ingantattun kayan aiki a sibitin.

“Gyare-gyaren zai kunshi gyara kayayyakin da ake da su, da kara gina sabbin gine-gine, da sanya na’urorin kiwon lafiya na zamani. Wadannan ayukka za su kara fadada asibitin don kara samun isassun dakunan jinyar marasa lafiya da kuma ingantattun kayan aikin kula da marasa lafiya.don kula da marasa lafiya."

No comments