Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Yan Ta'adda Na Yin Barazana Ga Rayuwa Ta -Gwamnan Katsina

Gwamnan jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa 'yan ta'adda na yi masa baranar za su kai masa hari.  Gwamnan ya bayyana...

Gwamnan jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa 'yan ta'adda na yi masa baranar za su kai masa hari. 

Gwamnan ya bayyana haka ne a wajen taron tsaron jihar, jiya Juma'a, taron da ya saba jagoranta a duk ranakun Juma'a a fadar gwamnatin da ke Katsina.

Gwamna Raɗɗa ya ce, "bayanin sirrin da mu ke samu, shi ne, ina cikin waɗanda 'yan ta'adda ke tunanin kai wa hari, wanda kuma wannan barazana ba za ta canja ni daga ƙoƙarin da na ke yi don ganin bayan su ba."

Ya ce, zai ci gaba da aiwatar da hanyoyi da dabarun da suka fito da su don ganin sun yi maganin Ta'addanci da sauran matsalolin tsoron da suka addabi jihar. 

Ya ce, "barazanar su a kai na, ba za ta sanya in yi sanyi ba, a wannan yunƙurin na gamawa da ta'addanci a jihar nan. Babu abin da zai same ni, domin Allah na tare da mu," in ji Gwamnan.

Shi dai wannan taro ya samu halartar duk shugabannin hukumomin tsaron da ake jihar, Shugabannin addini, Sarakuna da manyan ma'aikatan gwamnati.

 

No comments