Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yau Za A Rufe Rajistar Maniyyata Aikin Hajjin Bana Daga Jihar Kaduna

Hukumar kula da jin daÉ—in Alhazai ta jihar Kaduna ta na tunatar da Maniyyatan bana cewa a yau Litinin, 12 ga Faburairun nan na 2024 ne ranar...

Hukumar kula da jin daÉ—in Alhazai ta jihar Kaduna ta na tunatar da Maniyyatan bana cewa a yau Litinin, 12 ga Faburairun nan na 2024 ne ranar Æ™arshe ta yi wa duk wani maniyyaci rajista daga jihar. 

A cikin wata sanarwa da Kakakin Hukumar, Yunusa Mohammed Abdullahi ya sanya wa hannun, ta bayyana cewa hakan ya biyo bayan Æ™arin kwanakin da Hukumar ta Æ™asa ne ta Æ™ara a makon da ya gabata. 

Don haka sai Yunusa Mohammed Abdullahi ya jaddada cewa waÉ—anda suka samu kammala biyan kuÉ—aÉ—en nasu a yau ne kawai za su samu damar sauke faralin na bana daga jihar. Ya kuma jawo hankalin maniyyatan da su gaggauta kammala yin rajistar. 

Kakakin Hukumar Alhazan, ya kuma tabbatar wa da maniyyatan jihar cewa,  sun shirya tsaf don gudanar da aikin Hajji mai cike da nasara. Yana mai bayanin cewa, hatta waÉ—anda ba su ma fara biyan kuÉ—in ba, yanzu za su iya zuwa su yi rajistar a yau. Sai dai ya danganta da kujerun da suka rage. 

Sanarwar ta Malam Yunusa ta kuma bayyana cewa fiye da mutum 4,000 ne suka yi niyyar zuwa aikin na bana daga jihar Kaduna, wanda kuma Hukumar ta kammala duk shirye-shiryen da suka wajaba don ganin ta taimaka wa duk wanda ya nema. 

Ya ce, Hulumar kula da aikin Hajji ta Æ™asa NAHCON ta ware wa jihar Kaduna kujeru 6,004 daga cikin maniyyata 95,000 da ake sa ran za su sauke faralin na bana daga Nijeriya. 

"Bisa la'akari da ƙarancin kujerun da ake da su, Hukumar KSPWA ta na kira ga duk wani mai haramar zuwa aikin Hajjin bana, ya hanzarta yin rajista a yau don gudun kar a samu matsala," in ji sanarwar.

 

No comments