Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana mutuwar Shugaban Bankin Acces, Herbert Wigwe, a matsayin babban rashi ga harkar banki a Nijeriya. I...
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana mutuwar Shugaban Bankin Acces, Herbert Wigwe, a matsayin babban rashi ga harkar banki a Nijeriya.
Idan dai ba a manta ba, Herbert Wigwe ya mutu tare da matarsa da ɗansa a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a California kusa da kan iyakar Nevada da ke Ƙasar Amurka.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a Gusau ranar Lahadi, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana alhininsa kan rasuwar Herbert Wigwe da iyalansa.
A cewarsa, mutuwar Wigwe babban rashi ne ba ga iyalansa da abokansa kaÉ—ai ba, har ma da ’yan kasuwa a Æ™asar da ma nahiyar Afirka baki É—aya.
“A game da mutuwar Wigwe, na rasa aboki wanda ya ba da gudunmawa sosai ga harkar banki a Nijeriya.
“Herbert Wigwe ya bar giÉ“in da ba za a taÉ“a iya cike shi ba a harkar banki a Nijeriya ta hanyar jajircewarsa.
“Ya bayar da É—umbin gudunmawa ta hanyar Æ™warewarsa da ya amfani ’yan kasuwa da dama.
“Ina da dangantaka mai Æ™arfi da Wigwe tun zamanin da nake harkar banki.
“Allah ya ba dangi, abokai da abokan hulÉ—ar Wigwe haÆ™urin jure wannan babban rashi da ba za a taÉ“a mantawa da shi ba," in ji sanarwar.
No comments