Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Babu Sana'ar Da Ta Kai Ta Bola-jari Wajen Samar Da Aikin Yi Ga Matasa -Mr Bon

Daga Imrana Abdullahi Alhaji Murtala da ake yi wa laƙabi da Mr Bon, shi ne mataimakin shugaba a yankin Arewa ta Tsakiya na ƙungiyar Bola-jar...

Daga Imrana Abdullahi

Alhaji Murtala da ake yi wa laƙabi da Mr Bon, shi ne mataimakin shugaba a yankin Arewa ta Tsakiya na ƙungiyar Bola-jari ta NASWDEN, wanda kuma aka yi wa kyautar 'Super Agent'da ke gudanar da sana'ar sa a Kaduna, Abuja, Neja da Kano, ya bayyana cewa babban burin su shi ne ɗaga darajar sana'arsu da martabar u da dukkan abokan hulɗa da nufin samar da ci gaban pasa da na al'umma baki taya.

Mataimakin shugaban ya kuma bayyana cewa bisa la'akari da irin ayyukan da wannan ƙungiya ke samarwa, lallai sun gano cewa babu wata sana'a a duk faɗin ƙasar nan mai samar da ayyukan yi ga matasa kamar Bola-jari. 

Murtala ya bayyana hakan ne a wajen babban taron ƙungiyar NASWDEN da aka yi a ɗakin taro na NUT da ke yankin Mogadishi a garin Kaduna. Inda ya bayyana cewa a cikin pungiyarsu baki ɗaya babu wani da ke zauna gari-banza,  kowa ƙoƙari yake yi ya samar wa kansa da abin yi ta yadda za a samu nasarar da kowa ke buƙata, don haka a cikin ƙungiyar su babu wani mutumin banza.

"A cikin ƙungiyar mu, akwai Sarakuna, 'yan sanda da masu muƙamai da yawa, kai shugaban tsaro ma na Nijeriya baki ɗaya shi ne Uban punguyar NASWDEN. Wannan na oara fito da martabar masu wannan sana'a, kuma babu wasu maganganu saɓanin hakan da za a riƙa yaɗawa, sai ci gaba da samun nasara, tare da inganta tattalin arzikin pasa da na jama'a," in ji shi. 

Alhaji Murtala ya kuma ce akwai wani ƙalubalen da suke ƙoƙarin a ba su amsa a kansa a cikin Nijeriya, 'in banda Gwamnati, muna son a nuna mana wata sana'a ƙwaya ɗaya da ta fi sana'ar Bola-jari ba matasa aikin yi a Nijeriya? Mu a iya tunanin mu babu, saboda da akwai da an samu amsar tun da daɗewa.

"Muna yi wa Allah godiya cewa manyan da muka samu a cikin wannan sana'ar, kamar Alhaji Sani Jakara, haƙuri suka yi suka daure har Allah ya kawo matsayin da kan mutane ya waye game da wannan sana'ar, waccehar a yanzu kuma ake kiransu masu martaba. Don haka lallai haouri zai iya yin maganin komai."

Shi ma da ya ke zantawa manema labarai bayan kammala taron, Dokta Mubarak Labaran Liman, wanda shi ne muƙaddadhin shugaban ƙungiyar ta ƙasa, ya yi kira ga ɗaukacin 'ya'yan ƙungiyar da su ci gaba da yin haɗin kai da ƙokari a tafiyar da ƙungiyar gaba, tare da taimakon Juna.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron da ƙungiyar ta yi a Kaduna.

Dokta Mubarak Labaran Liman ya kuma miƙa  saƙo ga al'umma da kuma Gwamnati, inda ya yi kira da a ci gaba da ba ƙungiyar haɗin kai a kuma ci gaba da ba su tallafi ta yadda za su ƙara zage damtse wajen samar da taimako ga al'umma wajen aikin yi da tsaftace muhalli da nufin ciyar da sana'ar tasu gaba a kan batun sarrafa shara ta zama abin yin amfani a kodayaushe a duk faɗin ƙasar nan mai albarka.

"Muna kuma yi wa Allah godiya da aka samun yin wannan taron lafiya aka kammala lafiya har aka ƙaddamar, tare da rantsar da sababbin shugabanni na Jihar Kadun, kuma aka bayar da lambobin Yabo ga wasu mambobin jiha da ma wasu na wasu a mataki na oasa sakamakon irin ƙoƙarin da suka yi wa ƙungiya da tafiyar da sana'ar nan.

Barista Usman Salisu Jundullahi ne ya ranntsar da sababbin shugabannin na Jihar Kaduna da kuma na yankin Arewacin Nijeriya da suka haɗa da Abuja.

No comments