Daga Ibrahim Muhammad. Tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Ghari da ke jihar Kano, Hon. Aminu Idi Shuwaki ya bayyana cewa sauya sunan Ƙaramar H...
Daga Ibrahim Muhammad.
Tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Ghari da ke jihar Kano, Hon. Aminu Idi Shuwaki ya bayyana cewa sauya sunan Ƙaramar Hukumar Ƙunchi zuwa Ghari da aka yi a zamanin mulkin sa, shi kaɗai ya masa gagarumar nasara.
Hon. Shuwaki ya bayyana hakan ne da yake zantawa da 'yan jarida a Kano cikin makon nan, inda ya ƙara da cewa a matsayin sa na wanda ya shugabanci Ƙaramar Hukumar Ghari, Allah ya taimake su suka sami shawarwari da hatin kan mutane har Allah ya sa Ƙunchi ta zama Ghari.
Hon. Aminu Shuwaki ya ce, dama shi kusan daga gidan siyasa ya taso, abu ne da in ka karɓa, wata rana wani zai karɓa a wajenka. Kuma yana godiya ga Allah a mulkin sa ya tabbatar babu wata mazaɓa a Ƙaramar Hukumar Ghari da ba ta amfana daga ayyuka da ya yi ba a fannoni da dama.
Dan haka ya gode wa Allah bisa wannan dama da Allah ya ba shi na shekara Uku yana mulkin mutane, ya kuma gode wa al'ummar Ghari gaba ɗaya bisa haɗin kai da suka ba shi.
Hon. Aminu Idi Shuwaki ya ce wani abu da ya ke tunawa a shugabancin da ya yi, shi ne a lokacin da mahaifin sa ke Kansila a 1979 zuwa 80 lokacin mulkin Rimi, ya je wani ƙauye za a yi musu rijiya, a makon aka sauke su, bai samu damar yin rijiyar ba.
Ya ce, amma da Allah ya kawo shi a matsayin shugaban Ƙaramar Hukumar Ghari, a daidai wurin ya je ya haƙa musu rijiya aka sami ruwa. Ya ce, ba zai taɓa mantawa da wannan ba, wanda ko shi katai ya yi ya cika wa mahaifin sa burin sa a rayuwa.
No comments