Daga Ibrahim Muhammad Ƙungiyar tsofaffin ɗaliban makarantar Sakandaren 'yan mata ta Jogana, 'yan aji na 88 sun gunar da taron sad...
Daga Ibrahim Muhammad
Ƙungiyar tsofaffin ɗaliban makarantar Sakandaren 'yan mata ta Jogana, 'yan aji na 88 sun gunar da taron sada zumunci da karrama waɗanda suka bada gudummuwa akan ci gaban ilimi.
Taron Wanda aka gudanar a ɗakin taro na Kwalejin Fasaha ta Kano ya sami halartar da dama daga tsofaffin ɗaliban.
Shugabar ƙungiyar ta biyu ta 'yan ajin '88 kuma wacce ita ce Darakta a makarantar ilmi na musamman ta Tudun Maliki, wato 'Special Education School Tudun Maliki' Hajiya Umma Musa Abubakar ta ce mariyaya Hajiya Bilkisu Bayaro ita ce shugabar ƙungiyar ta farko.
Hajiya Umma ta nuna godiyar ta ga Allah da ya ba ta dama da tunanin assasa ƙungiyar ta Manhajar Whatsapp a 2014. Kuma ta sami haɗin kai daga tsofaffin daliban.
Ta ce, tunanin da ta yi na assasa ƙungiyar, shi ne ta lura da yawan su ba sa haɗuwa, ba sa ganin juna tun da suka gama makaranta, ga shi suna da ƙawazuci da ƙaunar juna. Saboda haka ta buɗe ƙungiyar akan tunani da ya haɗa da jaddada zumunci ingantacce mai ɗorewa.
Ta ƙara da cewa, sai kuma suka yi tunani na tallafa wa makarantar da kuma taimaka wa 'ya'yan marayu na cikin su, da kuma taima wa buƙatun junan su in wani abu ya taso, kama daga haihuwa, larura ce ta rashin lafiya, buki ko rasuwa da duk dai wani abin farin ciki da akasin sa suna ƙoƙari su saka hannu domin taimaka wa.
Hajiya Umma ta ce, daga tallafin da suka yi wa makarantar, akwai gyaran masallaci, kuma sun sami tallafin tsohon akanta janar na ƙasa, Ahmad Idris a gyaran, wanda miji ne ga ɗaya daga cikin 'yan ƙungiyar, wanda har sallar Juma'a ake yi yanzu a masallacin makarantar a Jogana.
Ta ƙara da cewa, sun tallafa wa bukin 'yar Hajiya Bilki, wacce aka saya mata kayan ɗaki. Suna kuma tallafa wa marayu, domin ko a wannan taro ma sun tallafa wa marayu guda 10 da tallafi na kuɗi.
Sannan akwai Malamai ciki har da tsohuwar shugabar makarantar da suka gama makaranta a hannun ta Hajiya Aisha Atiku, sun ba ta kyauta ta karramawa, da Hajiya Talatu da Malam Yusuf Da'u da Malam Sule Yahaya duk sun karrama su. Ita ma Dakta Hauwa an karramata, da Ahmad Idris.
Daga nan sai Hajiya Umma Musa Abubakar ta ja hankalin dukkan tsofaffin ɗalibai l, ba ma na makarantar Jogana ba kaɗai ba, akan cewa su sani akwai kule akan irin waɗannan ƙungiyoyi, amma abu ɗaya ne ake buƙata, tsayuwa ƙyam akan gaskiya da juriya da yin haƙuri a jagoranci, wanda in aka yi haka, to za a sami ci gaba da zaman lafiya.
No comments