Wata sabuwar amarya ’yar shekara 20 mai suna Aisha Aliyu da ke ƙauyen Nasarawa a Ƙaramar Hukumar Lafiya ta Jihar Neja ta kashe mijinta mai s...
Wata sabuwar amarya ’yar shekara 20 mai suna Aisha Aliyu da ke ƙauyen Nasarawa a Ƙaramar Hukumar Lafiya ta Jihar Neja ta kashe mijinta mai suna Idris Ahmadu.
Mazauna yankin sun shaida wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1 na safiyar ranar Litinin.
Majiyoyi da yawa sun ce ma'auratan sun yi aure ne a ranar 31 ga Disamba, 2023, daidai makonni shida da suka gabata.
Ɗaya daga cikin majiyoyin ta ce ma’auratan sun samu ’yar rashin fahimta ne da yammacin ranar Lahadi kuma an sasanta su kafin su kwanta, inda a tsakar dare mahaifiyar marigayin ta ji yana kururuwa.
“Lokacin da mahaifiyar ta fito tare da sauran mazauna gidan, sai suka tarar da shi cikin tafkin jininsa. Ya yi kokarin fita daga ɗakin amma ya faɗi a bakin ƙofa. Amma har ya zuwa yanzu, ba mu san inda matarsa ta ke ba,” inji majiyar.
Majiyar ta ƙara cewa, matar ta fara daɓawa mijin nata wuƙa ne a ƙirjinsa kafin daga bisani ta yanka masa maƙogwaro.
Da aka tambaye ta ko auren dole ne, majiyoyi sun ce ma’auratan sun shafe shekaru suna soyayya amma kafin a sanya ranar ɗaurin auren ta sauya ra’ayin ta auri wani.
“Amma ko da hakan, an warware matsalar. Sun fara wannan dangantakar tun daga makarantar sakandare kuma sun kasance tare daga wannan lokaci. Kafin a ɗaura auren ta ce ta daina sha’awar soyayyar, amma an warware matsalar, kuma ta amince a karshe, ba tare da sanin cewa tana da wani shiri ba. Ta ce tana da sabon mai neman auren ta,” inji shi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin.
“Yau 12/02/2024 (Litinin), da misalin karfe 1200 na safe, an samu labari cewa da sanyin safiya, wani Idris Ahmadu daga kauyen Nasarawa, ta hanyar Lapai, matarsa, Aisha Aliyu, mai shekaru 19/20 a wannan adireshin matarsa ta daɓa masa wuka har lahira.
“Kafin isowar ‘yan sanda a wurin, wadda ake zargin ya gudu zuwa wani wuri da ba a san inda ta ke ba, yayin da ake ci gaba da kokarin cafke wadda ake zargin ta gudu, amma an bazama nemanta ruwa-a-jallo,” in ji shi.
No comments