Daga Imrana Abdullahi, Kaduna Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Muktar Ramalan Yero ya tabbatar da komawar sa jam'iyyar APC, inda ya c...
Daga Imrana Abdullahi, Kaduna
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Muktar Ramalan Yero ya tabbatar da komawar sa jam'iyyar APC, inda ya ce ya canja sheƙar ne domin ya taimaka wa Gwamnatin jijar mai ci ta cimma burin ta na kawo ci gaban al'umma baki ɗaya.
Tsohon Gwamna Ramalan Yero ya bayyana hakan ne a wajen wani gagarumin taron manema labarai da ya kira a É—akin ganawa da jama'a da ke cikin gidan sa a Kaduna.
Ramalan Yero bayan ya yi wa Allah godiya ya ce, haƙiƙa tsawon watanni biyar ke nan da yake ta shawara, tare da ganawa da jama'a da kuma jam'iyyu daban daban-daban, "amma dai a yau na yanke hukuncin komawa jam'iyyar APC tare da ɗimbin al'umma ta baki ɗaya.
"Idan za a iya tunawa dai tun tsawon watanni biyar can baya na bayyana ficewa ta daga jam'iyyar PDP, amma ban faÉ—i inda zan nufa ba, ina ta tattaunawa da jam'iyyu daban-daban da suka zo wuri na suna shawarta ta, kodayake jam'iyyar APC ce ta fara zuwa wuri na a ranar da na bayyana ficewa ta daga jam'iyyar PDP, sai APC suka zo a ranar suna zawarcin in koma cikin jam'iyyar.
"To bayan a yau mun je gidan Gwamnatin Jihar Kaduna, mun kuma yi magana da Gwamna Uba Sani da jama'ar sa, na kuma shaida masu cewa gani ni da jama'a ta bayan mun kammala tattaunawa da dukkan shawarar da za mu yi, baki É—aya mun yanke shawarar komawa cikin jam'iyyar APC," in ji shi.
Ramalan Yero ya kuma ce sun samu kyakkyawar tarba da karamci a lokacin da suka je gidan Gwamnatin.
Haka, ya kuma bayyana wa manema labarai cewa ba ya koma APC ba ne domin ya yi takara, "mun koma ne domin taimaka wa Gwamnati a samu ci gaban yi wa al'umma abin da ya kamata, wanda daman can shi ne burin mu da na sauran jama'a," a cewar sa.
A cikin tawagar ta Ramalan Yero akwai waÉ—ansu ya'yana jam'iyyar LP da suka biyo tawagar tasa, su ma sun koma APC tare da sh, waÉ—anda suka haÉ—a da Maza da Mata.
Ɗaya daga magoya bayan Tsohon Gwamnan, Honarabul Nasiru Dogara daga Ƙaramar Hukumar Zariya ya bayyana cewa sun fice daga jam'iyyar PDP ne domin jaddada cikakken goyon baya da haɗin kai tare da nuna ana tare da tsohon Gwamnan, inda y ce, babu yadda za a yi ɗaki zai tashi ragaya ta zauna.
Nasiru Dogara ya shaida wa manema labarai haka ne, jim kaÉ—an bayan da suka kammala taron tattaunawa da tsohon Gwamna Muktar Ramalan Yero a gidan sa, inda suka amince da shawarar ficewa daga PDP.
No comments