Daga Magaji Sarki, Sakkwato Jam'iyyar PDP ta samu nasarar kayar da jam'iyyar APC a zaɓuka biyu cikin uku da aka saka gudanarwa a maz...
Daga Magaji Sarki, Sakkwato
Jam'iyyar PDP ta samu nasarar kayar da jam'iyyar APC a zaɓuka biyu cikin uku da aka saka gudanarwa a mazaɓar Majalisar Tarayya 1 da Majalisar Dokoki 2 a Sakkwato.
A zaɓen wanda kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukuncin sake gudanarwa a rumfuna 46 a Ƙananan Hukumomi huɗu; Umar Yusuf Yabo na jam'iyyar PDP da ke kan kujerar ya samu galaba a kan Abubakar Umar na jam'iyyar APC a mazaɓar Tarayya ta Yabo/Shagari.
A zaɓen wanda jam'iyyun biyu suka riƙa sayen puri'u kama daga dubu 20, 25, 30, 35 da injunan ban-ruwa da takin zamani, Yabo ya samu nasara da ƙuri'u 26, 829 a yayin da ɗan takarar APC ya samu ƙuri'u 26, 113 kamar yadda Baturen Hukumar Zaɓe, Farfesa Abubakar Abdullahi Bagudo ya bayyana.
Haka ma Matattarar Labarai ta labarto cewar Baturen zaɓen Majalisar Dokoki ta Jiha a mazaɓar Boɗinga ta Arewa, Farfesa Farouk Tambuwal ya bayyana Abubakar Magaji na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya samu nasara da tsaɓar ƙuri'a 6, 488, yayin da abokin karawarsa na APC, Yusuf Marafa Danchadi ya samu ƙuri'u 5, 893.
Sai dai Jam'iyyar APC ta samu nasarar karɓar kujerar Sulaiman Hantsi Romo, wakilin Tambuwal ta Yamma a Majalisar Dokoki ta Jiha wanda ke kan kujerar a inuwar jam'iyyar PDP.
Baturen zaɓen Farfesa Bayero Kasim Bukkuyum ne ya bayyana Bashir Ahmed na APC a matsayin wanda samu rinjaye da ƙuri'u 19, 315 a yayin da Romo na PDP ya samu ƙuri'u 19, 021.
A zaɓen dai, a bisa ga halin ƙunci da tsadar rayuwa da jama'a ke fuskanta an samu fitowar dandazon jama'a ba maska tsinke waɗanda suka riƙa musayar ƙuri'unsu da abin da za saka a baka.
No comments