Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnan Zamfara Ya Ƙaddamar Da Rabon Kayan Amfanin Gona Ga Manoman Ƙananan Hukumomin Bunguɗu Da Maru

A ranar Juma’ar da ta gabata ne Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ƙaddamar da rabon kayan amfanin gona ga manoman Ƙananan Hukumomin Bungud...


A ranar Juma’ar da ta gabata ne Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ƙaddamar da rabon kayan amfanin gona ga manoman Ƙananan Hukumomin Bungudu da Maru na jihar.

Ƙaddamar da rabon kayan a Bungudu da Maru, wani ɓangare ne na ci gaba da shirin farfaɗo da tattalin arziki na COVID-19 wanda FADAMA III ke taukar nauyi.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta bayyana cewa an fara rabon kayayyakin ne a ranar 3 ga watan Janairu a Gusau birnin jihar.

Ya ƙara da cewa Gwamna Lawal ya je Shinkafi, Gummi da Tsafe, inda ya paddamar da rabon kayan ga manoma.

“Yau Gwamnan ya ziyarci Ƙananan Hukumomin Bunguɗu da Maru domin raba muhimman kayayyakin noma da kayan amfanin gona ga manoma.

A Ƙaramar Hukumar Bunguɗu, Gwamna Lawal ya ce Ƙaramar Hukumar ta shahara wajen noma, kuma irin gudunmawar da ta bayar wajen haɓaka arzikin jihar Zamfara abin a yaba ne.

“Tare da ƙaddamar da wannan shiri a wannan Ƙaramar Hukumar a yau, muna samar da damammaki masu yawa ga al’ummomin da suke noma a wannan Ƙaramar Hukuma mai himma.

“Ina da yaƙinin cewa wannan shiri zai taimaka matuƙa wajen bunƙasa noman manoman mu, ta yadda za a rage raɗaɗin talauci da ƙalubalen da ke tattare da shi.

“Ƙari kan wannan yunƙurin, muna shirin gabatar da irin wannan ayyukan na ci gaban al'ummar mu, kamar haɗaɗɗiyar shirin kasuwanci. Wannan shirin zai ƙunshi ayyuka daban-daban na haɗin gwiwar noma, wadanda suka haɗa da kifaye, kiwon kaji, da sauran su.

“Bugu da ƙari, za ta ba da horo da fakitin farawa ga ƙananan 'yan kasuwa a sassa daban-daban, wanda zai ba da gudummawa sosai ga ƙoƙarin mu na inganta tattalin arzikinmu.

A Ƙaramar Hukumar Maru, Gwamnan ya sake bayyana cewa rabon tallafin zai magance zazzaɓin cizon sauro ta hanyar sabbin hanyoyi kamar kiwon kifin tilapia tare da samar da maƙudan kuɗaɗe ga waɗanda suka ci gajiyar tallafin ta hanyoyi daban-daban, domin babu shakka hakan yana inganta rayuwa.

“A bisa ƙudurin mu na inganta noma a Ƙaramar Hukumar Maru, gwamnati na za ta fara aikin gyaran madatsun ruwa na ƙasa, kuma an yi tanadin wannan a kasafin kudin 2024. Wannan shiri zai samar da guraben aikin yi ga manoma sama da 40,000 tare da taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da mutane sama da miliyan biyu a duk shekara.”

A yayin ƙaddamar da wannan aiki, sama da manoma 2,000 ne suka amfana a dukkanin Ƙananan Hukumomin Bunguɗu da Maru.

No comments