Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Zaɓen Cike Gurbi A Bauchi: PDP Ta Tafka Maguɗin Sayen Ƙuri'u - Sanatan Buba

Daga Khalid Idris Doya Sanatan Bauchi ta Kudu a Majalisar Dattawa, Sanata Shehu Buba Umar ya yi zargin cewa Gwamnati mai ci a jihar Bauchi (...

Daga Khalid Idris Doya

Sanatan Bauchi ta Kudu a Majalisar Dattawa, Sanata Shehu Buba Umar ya yi zargin cewa Gwamnati mai ci a jihar Bauchi (PDP) ta tafka muguɗi na sayen ƙuri'u a wajen masu jefa ƙuri'a a yayin zaɓen cike gurbin kujerun 'yan Majalisan Dokokin jihar Bauchi su huɗu.

Sanatan wanda ya shaida hakan a lokacin da ke ganawa da 'yan jarida dangane da yadda zaɓen ke gudana a jihar Bauchi ranar Asabar ɗin nan.

Ya ce tunin suka sanar da hukumomin tsaro ƙorafin da suke da shi na sayen ƙuri'u da kuma kame musu magoya baya da aka yi a yayin gudanar da zaɓen. 

Sai da duk da haka, Sanata Buba ya jinjina wa Hukumar zaɓe bisa yadda ta yi tsare-tsare masu kyau, sannan ya ce hukumomin tsaro su ma sun yi tsare-tsaren da suka dace na tabbatar da tsaro a yayin zaɓen.

Ya ce: "Daga rahotonnin da muke samu zaɓen na tafiya, sai dai 'yan abubuwan da ba za a rasa ba na koke-koke, shi ne muke ta karɓan rahotonni daga mazaɓu.

"Yawancin koke-koken da muka samu yawanci, ka san mu a jam'iyyar APC mu a nan jam'iyyar adawa muke, kuma muna fuskantar Gwamnati mai ci.

"Muna da labarin Gwamnati ta fito da kuɗi su na sayen ƙuri'a, kuma sun tura manya-manyan mutanen su an je ana tsorata mutanen mu ana sayen ƙuri'a."

Ya ƙara da cewa akwai ƙorafin da suke da shi na cewa an kama musu 'yan jam'iyyar APC a yankin Liman Katagum. 

Ɗan Majalisar ya nemi jama'a da su zaɓen bisa kwanciyar hankali ba tare da wani tashi hankali ba. Inda ya nuna gamsuwarsa kan yadda jama'a suka yi dafifi wajen fitowa a dama da su. 

An sake gudanar da zaɓen ne a kujerun 'yan Majalisun Dokokin jihar Bauchi su huɗu.

A zantawar sa da 'yan jarida kan wannan zargin, Kakakin jam'iyyar PDP, Alhaji Yayanuwa Zainabari ya ce babu wani gaskiya a wannan zargin. 

Ya ce babu wasu jami'i da suka tura rumfuna domin razana masu zaɓe, "Akwai jami'an tsaro a ko'ina kuma sun gudanar da aikinsu yadda ya dace. 

"Kawai ba su da pwarin gwiwa ne, shi ya sa suke wannan zargin," Ya shaida. 

No comments