A yau ɗin nan ne Allah ya yi Gwamnan farar hula na farko a jihar Yobe, kuma Tsohon Sanata daga jihar, Sanata Bukar Abba Ibrahim rasuwa yayin...
A yau ɗin nan ne Allah ya yi Gwamnan farar hula na farko a jihar Yobe, kuma Tsohon Sanata daga jihar, Sanata Bukar Abba Ibrahim rasuwa yayin da ya ke a ƙasar Saudi Arebiya don jinyar rashin lafiya.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya tabbatar da raauwar cikin wata sanarwa da Kakakin sa, Mamman Muhammad ya fitar, inda ya bayyana cewa za a yi jana'izar Sanatan ne a can Ƙasar Saudiyyar.
Ya kuma bayyana cewa Gwamna Mai Mala Buni zai ci gaba da karɓar gaisuwa a gidan gwamnatin jihar da ke Damaturu.
Marigayin shi ne maigidan Hon. Khadija Bukar Abba Ibrahim, 'yar Majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Ƙananan Hukumomin Gujba, Gulani, Damaturu da Tarmuwa. Ya rasu yana da kimanin shekara 75.
A ƙarshe Gwamna Buni ya sanar da cewa gwamnatin jihar za ta ɗauki dukkan ɗawainiyar jana'izar mamacin da kuma sauran shirye-shiryen karɓar gaisuwa.
No comments