Daga Musa Muhammad Hukumar kula da jin daɗin Alhazai ta jihar Kaduna ta shawarci maniyyata Hajjin bana su kammala biyan cikon kuɗin kujera...
Daga Musa Muhammad
Hukumar kula da jin daɗin Alhazai ta jihar Kaduna ta shawarci maniyyata Hajjin bana su kammala biyan cikon kuɗin kujerar da suka fara biya kafin nan da ranar 12 ga watan nan na Faburairu. Ta ce, wannan shawara ta zo ne sakamakon bayyana adadin kuɗin Hajjin bana da Hukumar Alhazai ta ƙasa NAHCON ta bayyana.
A cikin wata sanarwar da Kakakin Hukumar, Yunusa Mohammed Abdullahi ya fitar, ya ambato shugaban nasu, Malam Salihu S. Abubakar yana cewa da zarar maniyyaci ya kammala biyan kuɗin, to ya hanzarta zuwa wurin da ya yi rajista domin kammalawa. Yana mai cewa babu maniyyacin da zai hau jirgi ba tare da ya kammala biya ba.
Sanarwar ta ƙara sa cewa, akwai yiwuwar maniyyaci ya yi asarar kujerar sa muddin bai kammala biyan kuɗin ba, saboda Hukumar ta ƙasa ta ayyana wa'adin kammala biyan kuɗin.
"Wajibi ne duk wani maniyyaci ya karɓi takardar daga jami'in Alhazai na Ƙaramar Hukumar sa kafin ya je ya biya a banki," in ji sanarwar.
Ya ce, Malam Salihu ya kuma jaddada cewa ba a yarda wani ya yi wa wani rajista ba, kuma wajibi dattijai da masu lalura su je rajista da wani ɗan uwan sa a duk lokutan aikin Hajjin.
A 'yan kwanakin baya ne dai Hukumar Alhazai ta ƙasa, NAHCON ta sanar da cewa kowane maniyyaci daga yankin Arewa zai biya Naira Miliyan 4,699 a Hajjin bana, in ban da Borno da Adamawa.
Shugaban ya tabbatar wa da maniyyatan na bana cewa, Hukumar tasa ta haɗa hannu da Hukumar NAHCON da sauran masu ruwa da tsaki a harkar aikin hajji don ganin maniyyatan sun yi aiki cikin jin daɗi.
No comments