Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Jami’ar MAAUN Ta Rantsar Da Sabbin Ɗalibai 1,380 Na 2023/2024

Daga Musa Muhammad  Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN), dake Kano, ta yi nasarar kammala rantsar da sabbin ɗaliba...

Daga Musa Muhammad 

Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN), dake Kano, ta yi nasarar kammala rantsar da sabbin ɗalibai 1,380 da suka samu gurbin karatu na shekarar 2023/2024.

Bikin rantsar da ɗaliban karo na uku, ya gudana ne a ranakun Juma’a 2 ga Fabrairu da Asabar 3 ga Fabrairun 2024 a tagwayen ɗakin taro na Farfesa Abubakar Adamu Rasheed, inda baƙi da aka gayyata, ciki har da iyaye da sauran abokan arziki suka halarci taron.

Bikin rantsarwar na kwanaki biyu ya fara ne da ɗaliban Makarantun Shari’a da Kimiyyar Zamantakewa da Gudanarwa a rana ta farko, a yayin da ɗaliban Makarantun Kwamfuta, Kimiyyar Lafiya da Kimiyyar Jinya aka rantsar da su a rana ta biyu.

A nasa jawabin shugaban jami’ar MAAUN, Farfesa (Dr.) Mohammad Israr ya ce taron alama ce ta rantsar da ɗaliban da suka samu gurbin karatu a Jam'iar’ar a hukumance, kamar yadda hukumar kula da jami’o’i ta ƙsa (NUC) ta amince da su.

Ya taya ɗaliban murnar samun damar shiga Jami’ar sannan ya buƙace su da su rungumi kyakkyawan tarbiyya da kuma fuskantar karatunsu da gaske.

“Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya a Kano, yanzu ta faɗaɗa. Tana da hangen nesa na ganin ta bayar da abu mai inganci a fannin bincike, isar da abu a fannin kimiyya, shugabanci da gudanarwa.

“Fatan Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya a Kano, yana da girma. Ina mai kira ga kowa da kowa da ya haɗa kai da wanda ya assasa wannan jami’a da tawagarsa na ƙwararrun Malamai da masana domin ganin ci gaban Jami’ar tare da ƙara faɗaɗa ta,” in ji shi.

Ya ce jami’ar tana karantar da kwasa-kwasai waɗanda kawai da ke da kimar kasuwanci ga ɗalibai, yana mai jaddada cewa tsarin koyarwa a jami’ar ya shafi sanya wa ɗalibai sha’awar harkokin kasuwanci da hanyoyin dogaro da kai.

A nasa jawabin, wanda ya kafa gamayyar jami’o’in MAAUN kuma shugaban jami’o’in, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya ce MAAUN jami’a ce ta duniya domin akwai ɗalibai daga wasu kasashe ciki har da ƙasar Sin.

Ya shawarci ɗaliban da aka rantsar da su fuskanci karatunsu da gaske, inda ya ce duk wanda ya kasa, to za a nuna masa hanyar barin jami’ar.

Ya ce ya kamata sabbin ɗaliban su yi wa kan su murna na samun gurbin shiga jami’a, inda ya ce, domin shaidar kammala karatu a jami’ar ta MAAUN an amince da ita a ƙasar Amurka.

Farfesa Gwarzo ya ce ya kamata ɗaliban da suka samu gurbin karatu su kuma yi alfahari da kasancewarsu na shiga cikin iyalin MAAUN domin ya ce za su ci dimbin gajiyar jarin ilimi da na abin duniya.

Ya ce jami’ar ta himmatu wajen samar da ilimi mai inganci domin samar da ƙwararrun ɗaliban da za su bayar da gudunmawarsu wajen ci gaban nahiyar Afrika da ma duniya baki ɗaya.

A sakon sa na fatan alheri, mataimakin shugaban jami’ar Franco-British International University (FBIU) a Kaduna, Farfesa Abdullahi Mohammad Sabo ya shawarci ɗaliban da su tsara manufarsu tun daga ranar nan da aka rantsar da su domin su kammala karatunsu da sakamako mafi kyawu.

Ya kuma hori ɗaliban da aka rantsar da su kasance masu kyakkyawan hali domin kiyaye sunan Jami’ar tare da cimma burinsu na rayuwa.

Shi ma a saƙon sa na fatan alheri, mataimakin shugaban jami’ar MAAUN a Maraɗi, Dakta Shu’aibu Tanko ya ce tasirin MAAUN ba kawai a iya karatu ba ne har ma da zuba ma basirar da za ta bai wa ɗalibai damar dogaro da kai bayan kammala karatunsu.

“Kun zo nan ne don samun mafi kyawu domin ku tsaya da kafafunku bayan kammala karatu,” in ji shi.

Shi ma a saƙon sa na fatan alheri, Mataimakin Shugaban Jami’ar NorthWest Sakkwato, Farfesa Ahmad Maigari Ibrahim wanda ya samu wakilcin Dr Rabi’u Muhammad ya shawarci ɗaliban da suka samu gurbin karatu da su guji yin abubuwan da za su iya bata sunan su da na jami’ar.

Mataimakin shugaban jami’ar MAAUN Kano ɓangaren gudanarwa, Dakta Habib Awais Abubakar wanda ya jagoranci gabatar da rantsarwar a lokacin bikin rantsar da ɗaliban, shi ne ya rantsar da sabbin ɗaliban.

Sauran ma’aikatan Gudanarwa da suka halarta a yayin bikin sun haɗa da; Mataimakin Jami’ar ɓangaren rayuwar makaranta (Campus Life), Dr. Hamza Garba da Daraktan tsare-tsare na ilimi da tabbatar da inganci, Dr. Nura A. Yaro.

Sauran sun haɗa da Shugaban ofishin hulɗar kasa da kasa na MAAUN (International Office), Engr. Bashir Garba, Shugabannin Makarantu, Shugabannin sashe, Jami’an tsaro da kuma baƙi da aka gayyata da dai sauransu.

No comments