Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gidan Damben Diye-Diye Abuja Barazana ne Ga Tsaro -Sarkin Malaman Abuja

Daga Hussaini Yero Sarkin Malaman Abuja , kuma babban Limamin Masallacin Juma'a na garin Diye-Diye da ke Abuja, Shaikh Muhammad Alkwanda...

Daga Hussaini Yero

Sarkin Malaman Abuja , kuma babban Limamin Masallacin Juma'a na garin Diye-Diye da ke Abuja, Shaikh Muhammad Alkwandawi ya bayyana cewa, barin Gidan Damben Diye-Diye zuwa Dakwa barazana ne ga matsalar Tsaro da bada gudunmuwa wajan lalata tarbiyyar alumma.

Sarkin Malaman ya bayyana haka ne a huÉ—ubarsa ta Juma'arda ta gabata a Masallacin Juma'a na Diye-Diye da ke Abuja.

Shehin Malammin ya bayyana cewa, a lokacin da wasu masu kishin addinin Musulunci suke sayen gidan fasadi da gidajan Shaye-ShayAen barasa suna maida su masallatai da Makarantun a Diye-Diye, sai ga shi wani ya buÉ—e gidan Dambe da yake tattara masu É“arna ta kowane janibi, kuma hukuma ta yi shiru akai, amma tana rusa matsugunin raunana da canbobi da marasa Galihu ke ciki. 

"Maimakon rushe Canbobi, kamata ya yi gwamnati ta rusa gidan Damben da ke tattara masu laifuka da yake gurɓata tarbiyyar al'umma.

Haka zalika ma, Sarkin Malaman ya jadda cewa,a ƙoƙarin da Shugabanin ƙasa, Bola Ahmad Tunibu da mataimakisa Kashim Shatima ke yi na ganin an samar da zaman lafiya da yaƙi da masu miyagun ɗabi'u, ya kamata mu rufa masa baya, kuma duk wuraren da al'umma ke ganin baraza ce ga da tsaro, ya kamata gwamati ta ɗauki mataki akai .

"Akan haka na ke kira da babbar murya ga masu ruwa da tsaki a ɓangaren tsaro da su gagguta rufe gidan Damben Diye-Diye zuwa Dakwa, haka zai taimaka wajen samar da tsaro da kuma inganra rayuwar matasa."

 

No comments