Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Muna Sa Ran Rufe Kasuwannin Canjin Kuɗi Zai Taimaka Mana -'Qungiyar 'Yan Canji

  Daga Musa Muhammad Alhaji Abduljalil Usman, shi ne Kakakin ƙungiyar masu hada-hadar kuɗaɗen ƙasashen waje ta 'Association of Forex Tr...

 

Daga Musa Muhammad

Alhaji Abduljalil Usman, shi ne Kakakin ƙungiyar masu hada-hadar kuɗaɗen ƙasashen waje ta 'Association of Forex Traders,' reshen jihar Kaduna, waɗanda kuma ake kira da 'yan canji. A wata tattaunawar da suka yi da wakilin mu a ofishin sa da  ke Hotal ɗin Hamdala, ya bayyana cewa suna sa ran matakin da ƙungiyar su ta ƙasa ta ɗauka na dakatar da hada-hadar kuɗaɗen zai taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar da suke fuskanta ta ƙarancin kuɗaɗen ƙasashen wajen da suke fama da ita a kasuwannin qasar nan.

Yana mai cewa ƙarancin Dalar Amurka a kauwannin nasu ne ya sabbaba wannan muguwar tsadar da Dalar ta yi a kasuwannin.

Kakakin ƙungiyar, wanda ya yi magana a madadin shugaban ƙungiyar ta jihar Kaduna, Alhaji Ɗalhatu Haruna Jumare, ya bayyana cewa a halin da ake ciki, manyan kasuwannin nasu da ke Abuja, Legas, Kano da Kaduna, duk sun dakatar da hulɗar canjin kuɗin, bisa dalilin tashin gwauron zaɓin da Dalar Amurka ta yi a ƙasar nan.

Alhaji Abduljali ya bayyana manyan dalilan da suka sabbaba wannan matsala da cewa, "Gaskiya halin da ake ciki na rashin isassun kuɗaɗen duniya a hannun 'yan kasuwar mu, ba zai yi wa duk wani mai hankali daɗi ba, musamman yadda kuɗaɗen ke tashin gwauron zabi a kullum, wanda hakan ta samo asali ne daga ƙarancin kuɗaɗen shigowa da gwamnati ke samu daga ƙasashen wajen.

"Kamar yadda kowane lokaci mukan yi bayani, mafi yawancin duk wata hada-hada da ake yi ta ƙasashen Duniya, kowace ƙasa ba da kuɗaɗen ta ta ke yi ba, akwai abin da a Turance a ke ce ma 'Centran corrency' ko kuma Bench Mark', wanda ya ke shi ne ma'auni na ƙarfin tattalin arzikin kowace ƙasa. Wannan ma'auni kuwa, shi ne Dalar Amurka, wanda ita ce makarɓiya, ita ce kuma ma'auni na tattalin arzikin kowace ƙasa.

"Misali, mutumin da ke nan Nijeriya, ba zai sanya Naira a aljihu ya hau jirgi ya ce zai kashe a duk ƙasshen da ya je ba, wata ƙasar ma ba su san mene ne Naira ba. Saboda haka ita wannan Dalar, ita ce ake amfani da a duk inda ka shiga a duniya. Wannan yana nuni da cewa duk ƙasar da ta sayar da wani abu a duniya, to tana da Dalar da ke shigowa, haka ma mai zuwa ya sayo, shi ma sai ya nemi Dala.

"To, amma saɓanin mu abin da muka samu kan mu a nan, abu ɗaya muke fitarwa, wanda ya ke shi ne ɗanyen mai, shi kaɗai muke fitarwa a Kasuwannin duniya. Sai ya zamana kuma ga shi ƙasashe da yawa yanzu sun fara amfani da motoci masu amfanin da hasken rana, wanda ya sa bupatuwar ɗanyen man ya ragu sosai a kasuwar Duniya, kuma farashin sa babu yawa."

"Saboda haka wannan ya sanya kuɗaɗen da muke samowa daga wajen sun ragu sosai,  sannan kuma  buƙatuwar da muke da shi ga Dala ɗin, abin ya ƙaru, wanda wannan nauyin ya yi ma  Dalar yawa, buƙatuwar ta ya ƙaru, sannan shigowar ta ya ragu, don haka  nauyi ya yi wa Dalar yawa.

"Yanzu misali, a da akwai  wata dama da babban bankin ƙasar nan ya ba ƙananan bankuna, cewa idan mutum zai fita waje don neman lafiya, Babban bankin ya amince wa wannan banki su ba wannan mutumin Dala. Haka  ma wanda zai tafi karatu ƙasar waje, haka shi ma mai son fita yawon buɗe ido, duk babban bankin ya amince wa ƙananan bankuna su ba su Dala, muddin sun cika duk sharuɗɗa. To, Waɗannan abubuwa nauyin su ya ragu a kan mu 'yan kasuwa, a wancan Lokacin.

"To, amma hawan wannan gwamnati, wata kila saboda kuɗaɗen ba sa shigo mata yadda ya kamata ne, sai ta rufe waccan ƙofar da babban bankin ya ba ƙananan bankuna. Saboda haka sai nauyin duk ya dawo a kan mu 'yan kasuwa.

"Ka ga 'yan kasuwa masu fita domin sayo kaya, duk sun dogara da mu ne. Saboda haka zuwan wannan gwamnatin, duk sai nauyin ya dawo kan mu 'yan kasuwa. Yanzu kashi casa'in cikin ɗari na samar da wannan Dalar, duk yana kan mu ne, shi ya sa abin ya taru ya yi mana  yawa.

Kuma ka san a al'ada, duk lokacin da ake neman abu a kasuwa, to dole ne ya yi tsada, haka kuma duk lokacin da abu ya yawaita a kasuwa, dole zai yi arha. Wannan ne babban abin da ya sa Dala ta yi wannan mummunar tsadar."

Saboda haka sai Alhaji Usman ya bayar da tabbacin cewa suna sanya tsammanin cewa wannan mataki da suka ɗauka na rufe kasuwannin su, zai taimaka wajen kawo sauƙi a wannan hali da ake ciki, "muna gwaji ne mu ga, shin wannan matakin zai haifar mana da ɗa mai ido!

No comments