Ƙungiyar Ƙwadago a Jihar Zamfara ta karrama gwamna Dauda Lawal da lambar yabo na 'Gwamna Mafi Tausayi'. A ranar Alhamis ɗin da ta ga...
Ƙungiyar Ƙwadago a Jihar Zamfara ta karrama gwamna Dauda Lawal da lambar yabo na 'Gwamna Mafi Tausayi'.
A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne ƙungiyoyin ƙwadagon Nijeriya na NLC da TUC suka miƙa wa gwamnan lambar yabo a fadar gwamnati da ke Gusau.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa kyautar da ƙungiyar ƙwadago ta bada ya nuna irin nasarorin da gwamna Lawal ya samu a cikin watanni takwas na farko a kan karagar mulki.
A cewarsa, tun da farko gwamnatin jihar Zamfara ta sanya jin daɗin ma’aikatanta a kan gaba.
Gwamna Dauda Lawal ya ce, samun karramawar da ƙungiyar ƙwadago ta yi masa zai kƙra masa ƙwarin gwiwa wajen ƙara himma wajen kyautata rayuwar ma’aikata.
“Gwamnatina za ta ci gaba da jajircewa wajen inganta rayuwar al’ummar Zamfara, ma’aikata, da kuma ci gaban kowa. Muna da tsare-tsare da dama na inganta jin daɗin ma’aikatanmu, wafanda tuni aka fara aiwatar da wasu daga cikinsu.
“Mun warware matsalar rashin albashi da muka gada daga gwamnatin da ta shuɗe, kuma mun samu damar samar da albashin watanni 13 a karon farko a tarihin jiharmu. Bugu da ƙari, mun kafa wani kwamiti da zai daidaita bashin da ake bi na waɗanda suka yi ritaya daga shekarar 2011 zuwa yau, wanda ya kai Naira biliyan 13.4.
“Kwamitin ya riga ya yi nisa tare da tantance bayanan da ƙananan hukumomi da hukumar fansho ta jiha suka gabatar tare da tantance waɗanda suka ci gajiyar aikin.
“Masu ritaya daga gwamnatocin jihohi da na ƙananan hukumomi za su karɓi kuɗaɗen da ake bin su kamar yadda aka fara biyan su.
"Mun yi alƙawarin yi wa al'ummar Zamfara hidima, domin ceto da sake gina jihar. Kuma abin da gwamnatina ta ke yi ke nan. Ina so in gode muku da wannan karramawar da ku ka ba ni, domun tana da kima a gare ni."
Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya reshen Zamfara, Kwamared Sani Halliru da na ƙungiyar ’yan kasuwa, Kwamared Sa’idu Mudi, sun ce ƙungiyar ta baiwa gwamna Dauda Lawal lambar yabo ne saboda jajircewarsa na ci gaba da kyautata rayuwar al’umma da ma'aikatan Zamfara.
Shugabannin ƙungiyar ƙwadagon sun kuma bayyana cewa wannan shi ne karo na farko a tarihin jihar da wani gwamna ke nuna irin wannan kima ga ma’aikata.
No comments