Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnan Zamfara Ya Yi Alƙawarin Tallafa Wa Waɗanda Gobarar Kasuwar Gusau Ta Shafa

Gwamna Dauda Lawal ya yi alƙawarin bayar da duk wani tallafi da ake buƙata da taimako ga waɗanda gobarar babbar kasuwar Gusau ta shafa.   A ...



Gwamna Dauda Lawal ya yi alƙawarin bayar da duk wani tallafi da ake buƙata da taimako ga waɗanda gobarar babbar kasuwar Gusau ta shafa.
 
A daren ranar Talata ne wata gobara ta tashi a babbar kasuwar Gusau, inda ta yi sanadiyyar mutuwar mutum guda da shaguna sama da 50.


Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce a lokacin da ake tantance irin ɓarnar da gobarar ta haifar, gwamna Lawal ya sha alwashin taimakawa waɗanda lamarin ya shafa.
 
Ya ƙara da cewa, Gwamna Lawal ya tabbatar wa mutanen da abin ya shafa da iyalansu cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa don rage musu raɗaɗin da suke ciki da kuma taimaka musu wajen farfaɗowa daga asarar da suka tafka.
 
Da yake jawabi ga wafanda gobarar ta shafa a babbar kasuwar Gusau, gwamnan jihar Zamfara ya jajanta wa shugabannin kasuwar bisa rasuwar mutum ɗaya a yayin afkuwar lamarin.

“Ina miƙa ta’aziyyata ga shugabannin kasuwar da kuma iyalan mamacin da ya rasu sakamakon gobarar da ta faru a baya-bayan nan.
 
“Tun kafin afkuwar gobarar da ta faru, na kafa wani kwamiti da zai gudanar da cikakken bincike kan yadda gwamnati za ta sa baki domin inganta kasuwannin jihar nan da kuma bunƙasa su.
 
"Gwamnatina ta ƙuduri aniyar tallafawa waɗanda gobarar ta shafa kuma za ta binciko hanyoyi daban-daban don rage musu asarar."
 
Kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar Zamfara, Abdulrahman Tumbido, ya bayyana cewa gwamnati ta bada ɗaukin gaggawa domin shawo kan gobarar da kuma kashe ta.
 
Da yake mayar da martani a madadin waɗanda abin ya shafa, Shugaban Kasuwar Gusau, ya yabawa gwamnatin jihar Zamfara bisa gaggauwa da ɗaukar mataki bayan faruwar lamarin.


No comments