Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gidauniyar 'A A Charity' Ta Karrama Kwamishinar Mata Ta Sakkwato

Daga Imrana Abdullahi Sakamakon irin ƙoƙari da jajircewa wajen ganin rayuwar Mata da Yara da sauran al'umma, suka sanya Gidauniyar taima...


Daga Imrana Abdullahi

Sakamakon irin ƙoƙari da jajircewa wajen ganin rayuwar Mata da Yara da sauran al'umma, suka sanya Gidauniyar taimaka wa marayu, Gajiyayyu da sauran mabuƙata ta "A A Charity" ta Karrama Kwamishinar ma'aikatar da ke kula da harkokin mata ta Jihar Sakkwato, Hajiya Hadiza Ahmed Shagari.

A wajen babban taron ƙaddamar da shugabannin Gidauniyar da kuma raba tallafi da kayan karatu da aka raba wa 'yan makaranta marayu da kuma gajiyayyu a Kaduna ne aka bayyana haka, wanda wakilan Kwamishinar suka karɓa a madadin ta.

Hajiya Dokta Aminatou Abdoulkarim Muhammad ita ce shugabar Gidauniyar, ta kuma bayyana dalilin da ya sa ta ke aiwatar da ayyukan jin ƙai, inda ta tabbatar da cewa ta na yin aikin ne saboda tausayi, sakamakon irin yadda ta ga halin da waɗansu mutane ke ciki na rayuwa.

Ta ce, Musamman matan da suka rasa mazajen su, wasun suna cikin wani halin mawiyaci na rayuw, don haka suna tsananin bupatar taimakon al'umma.

Hajiya Uwani ce ta karɓi karramawar a madadin Kwamishinar ma'aikatar kula da harkokin mata ta Jihar Sakkwato, Hajiya Hadiza Ahmed Shagari.

No comments