Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Yan Ta'adda Sun Kashe Basarake, Tare Da Yin Awon Gaba Da Matar Sa

  'Yan Bindiga sun kai wani mummunan hari Fadar Olukoro da ke yankin Koro a Ƙaramar Hukumar Ekiti a Jihar Kwara, inda suka kashe basarak...

 

'Yan Bindiga sun kai wani mummunan hari Fadar Olukoro da ke yankin Koro a Ƙaramar Hukumar Ekiti a Jihar Kwara, inda suka kashe basaraken yankin, Janar Segun Aremu (mai ritaya), tare da yin awon gaba da matar sa da wasu mutum biyu.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, Toun Ejire-Adeyemi, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar da safiyar ranar Juma’a.

A cewar ta, “Ana ci gaba da gudanar da bincike don kama watanda suka aikata wannan laifin.

Kakakin 'yan sandan ta ce, “Muna tabbatar wa jama’a cewa, ba za a ƙyale watanda suka aikata wannan laif, ba tare da an gurfanar da su ba.

“An tsaurara matakan tsaro a yankin Koro, don tabbatar da tsaro da walwalar mazauna yankin”.

Ta ce, Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Victor Olaiya, Ya buƙaci jama’a da su kwantar da hankalin su, domin rundunar na aiki tuƙuru don cafke masu laifin, tare da gurfanar da su a gaban kotu.”

Gwamnan jihar, AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana kisan Basaraken a matsayin abin tashin hankali, abin tsoro, kuma abin Allah-wadai.

AbdulRazaq, ya kuma buƙaci jami’an tsaro da kada su yi ƙasa a gwiwa wajen gano ‘yan bindigar da suka kashe Basaraken.

“Tabbas za mu gano waɗanda suka aikata laifin, kuma za mu tabbatar da cewa wannan shi ne laifin su na ƙarshe da za su aikata.

“Ina miƙa ta’aziyya ta ga al’ummar Koro. Muna cike da baƙin ciki,” cewar Gwamnan.

No comments