Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kwamitin Zagayen Mauludi Na Qafilatul Mahabbah Ya bai Wa Majinyata 200 Tallafi

Daga Hussaini Yero, Funtua  Kwamitin Zagayen Maulidi na Ƙaramar Hukumar Funtuwa, haɗin gwiwa da Qafilatul Mahabbah Reshen Funtuwa sun raba t...


Daga Hussaini Yero, Funtua 

Kwamitin Zagayen Maulidi na Ƙaramar Hukumar Funtuwa, haɗin gwiwa da Qafilatul Mahabbah Reshen Funtuwa sun raba tallafi kuɗi da a binci ga majinyata 200 da ke kwance a Babban Asibitin Funtuwa .

Shugaban Kwamitin Zagayen gayan Maulidin, Malam Bashir Muhammad Kin, da Shugaban Ƙungiyar Qafilatul Mahabbahl,Br. Ahmad Tijjani Magaji Funtua sun bayyana cewa, sun shirya wannnan ziyara ne ga waɗanda Allah ya jarabta da rashin lafiya domin jajanta masu da kuma ba su tallafin kuɗi da Abinci, albarkacin murnar haihuwar Manzan Allah (SAW) .

"Bayan Zagayen Maulidin, da kuma na zaune da muke yi, sai kuma wannan ziyara ta marasa lafiya a Asibitici, da Gidan Gyaran hali, duk muna kai ziyarar Maulidi ga 'yan Uwa mu da suka gamu da jarabawar," in ji shi.

Shi ma a nasa jawabin, Babban Limamin Masallacin Juma'a na Funtuwa, Liman Abudurrahmman Jibril, ya Jagorancin Malamai wajen yin nasiha ga majinyatan da masu jinyar su.

Liman da sauran Malaman da suka haɗa da Malam Ahidu, Shugaban Ƙadiriyya na Funtuwa, da Malam Yusif Lawandi, da Khilfa Shehu Halilu Ɗandume, da Dr Kabir Shehu Rufai Bakori ne suka Jagorancin bada tallafin da kuma yin nasiha ga majinyatan.

Darakta DNC, Abdullahi D Umar ya bayyana godiyar su a madadin Hukumar gudanarwar Asibitin akan wannan tallafin da aka ba masara lafiya da ke kwance a Asibitin.

DNC Umar ya kuma tabbatar da cewa wannan tallafin zai taimaka masu sosai ga su majinyatan na kuɗi da Abinci.

Daraktan ya kuma jinjina wa wannan gamayyar Ƙungoyiyi da suka ba da wannnan tallafin albarkacin haihuwar Manzan Allah SAW.
 

No comments