Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ma'aikatar Ƙwadago Ta Tarayya A Jihar Kano Ta Gudanar Da Taro Kan Sanin Dokoki

  Daga Ibrahim Muhammad, Kano Kwanturola mai kula da ofishin jihar Kano na ma'aikatar ƙwadago ta tarayya, Alhaji Abdullahi Aliyu ya bayy...

 
Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Kwanturola mai kula da ofishin jihar Kano na ma'aikatar ƙwadago ta tarayya, Alhaji Abdullahi Aliyu ya bayyana cewa lokaci zuwa lokaci suna shirya taro don ƙara bayyana irin yanayin ayyukan su da abokan ayyukan su na kamfanoni, wani lokaci kuma da Gwamnatoci don ƙara fahimtar juna da zaman lafiya tsakani masu kamfani da ma'aikatan su.

Shugaban ya bayyana haka ne a yayin taron da suka gudanar da masu kamfanoni da ma'aikata a ranar Asabar. Ya ce suna taron ne don tabbatar da masu kamfani suna bin doka da kula da rayuwar ma'aikata yadda ya kamata.


Ya ƙara da cewa, ita Gwamnatin tarayya da duk wata hukuma, abin da ta sa a gaba kafin komai  shi ne zaman lafiya, wanda yana da muhimmanci Kamfanoni da abokan hulɗa, ma'aikata ya zamanto suna zaune lafiya, wanda shi ne zai kawo ci gaba.

Daga nan ya yi nuni da cewa, ba a hana ɗan adam yin kuka ba, illa dai duk yadda ka kai da ƙoƙarin yin gyara wani wajen ma idon ka ba zai kai ba, balle ka yi wani abu, amma suna yin iya  ƙoƙarin su su  tabbatar haƙƙoƙin da Gwamnati ta ɗora  musu sun bi.

Ya ce, mahalarta taron yawanci manajoji ne na kamfanoni da ƙananan ma'aikata da matsakaita da manya, ana haɗa su tare ne saboda in kana so ka tabbatar da nasarar abu, to ka haɗa kowa, shi ƙaramin ma'aikaci idan yana da ƙorafi wani lokaci yana neman inda zai faɗa, in ka yi nasarar haɗa shi da babban ma'aikaci, in ya yi ƙorafi a inda yake ganin yana da damar ya yi, ko ba ka gaya wa babban ma'akacin ƙorafin ba, to wata dama ce  da babban ma'aikaci  zai san ashe wani abu yana faruwa.

Ya ce irin wannan taro suna tattara matsaloli su rubuta rahoto su aika hedkwatar domin a ɗauki mataki da za a sa a doka don kyautata tsarin tafiyar da harkar ƙwadago tsakanin kamfani da ma'aikata.

Taron kuma na haɗin gwiwa ne tsakanin su da kamfanonin da ake gabatar da shi don amfanar da su kamfanin da masu aikin da Gwamnati wanda ita ribar ta ta ga ƙasa, ta zauna lafiya da samun ci gaba na tattalin arziki, su kuma masu kamfani su na yi ne don riba, don su taimakawa ƙasa ta ci gaba, a samar da aikin yi. Shi kuma ma'aikaci yana yi ne don shi ma ya anfanar da  iyalin sa, ya kyautata wa  harkokin rayuwar sa.

Da yake karin haske game da wannan taron, ɗaya da ga jami'an ma'aikatar ƙwadago ta tarayya. Murtala Haruna Abdullahi, ya bayyana cewa suna shirya taron ne domin faɗakarwa, horarwa  da ƙara wa juna sani ta yadda masu ɗaukan ma'aikata da ma'aikatan, musamman a  masana'antu da sauran wuraren aiki za su kasance a wayar musu da kai kan yadda za su yi  aiki, tare da kyautatawa a tsakanin su yadda doka ta tanada.
 

No comments