Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƙin Karɓar Toshiyar Baki Daga Kidinafas: Shugaban Ƙaramar Hukuma Ya Karrama DPO

Daga Musa Muhammad Shugaban Ƙaramar Hukumar Kagarko ta jihar Kaduna, Hon. Nasara Rabo ya karrama babban jami'in 'yan sanda DPO, mai ...

Daga Musa Muhammad

Shugaban Ƙaramar Hukumar Kagarko ta jihar Kaduna, Hon. Nasara Rabo ya karrama babban jami'in 'yan sanda DPO, mai kula da yankin Tafa, Idris Ibrahim da kyautar Naira Miliyan Ɗaya bisa nuna kishin al'umma na ƙin karɓar cin hanci daga wani madugun mai garkuwa da mutane. 

Shugaban Ƙaramar Hukumar ya sanar da haka ne cikin wata takardar yabo da jinjina da ya aika wa DPO ɗin cikin makon nan. 

Ya ce, DPO Idris ya kama wani mai garkuwa da mutane a ranar 22 ga watan Janairun nan da ya gabata, inda ɗan ta'addan ya yi masa tayin maƙudan kuɗaɗe in har ya dagula lamarin ta yadda za a sake shi, amma saboda kishin ƙasa ya ƙi karɓar kuɗin, tare da nuna cewa a bar doka ta yi aikin ta. 

Hon. Rabo ya ce, “Wannan abu da ya yi, ba wai rundumar 'yan sanda kaɗai ya jawo wa mutunci ba, har da al'ummar Ƙaramar Hukumar Kagarko, jihar Kaduna da ma Nijeriya gaba ɗaya, duk ya ja masu mutunci. 

"Wannan yana nuni ke nan da cewa in dai akwai mutanen kirki irin ku a aiki, to lallai babu shakka za a ga bayan ta'addanci da sauran matsalolin tsaron da suka dabaibaye al'umma a yau. 

“Bisa wannan ne, 'yan Majalisa ta da sauran ma'aikatan Ƙaramar Hukumar Kagarko mu ke ba ka wannan shaidar karramawa, tare da kyautar Naira Miliyan Ɗaya don mu ƙara maka himma da jajircewa wajen yaƙi da ɓata-gari a wannan Ƙaramar Hukuma da ma ƙasar baki ɗaya. 

Daga nan sai Shugaban Ƙaramar Hukumar ya jawo hankalin sauran jami'an tsaro da su dage wajen ƙin amincewa da haɗa baki da maɓarnata wajen gudanar da aikin su.

A ƙarshe ya roƙi Allah ya ƙara wa DPO Idris himma da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyar al'umma.

 

No comments