Daga Imrana Abdullahi Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Katsina ta sanar da ranar 15 ga watan Fabrairu, 2025 a matsayin lokacin da za a ...
Daga Imrana Abdullahi
Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Katsina ta sanar da ranar 15 ga watan Fabrairu, 2025 a matsayin lokacin da za a gudanar da zaɓen shugabannin Ƙananan Hukumomi da Kansiloli a duk faɗin Jihar.
Shugaban Hukumar, Lawal Faskari ne ya bayyana hakan a wajen wani taron manema labarai da ya kira a Katsina, wanda ya samu halartar wakilan jam'iyyu da jami'an tsaro a Jihar.
Ya ce an yi wannan sanarwar ne domin tabbatar da abin da doka ta tanadar a harkar zaɓe.
A lokacin zaɓen, ana sa ran samun zaɓen shugabannin Ƙananan Hukumomi 34 da Kansiloli 361 a ɗaukacin Jihar.
No comments