Daga Musa Muhammad A halin da ake ciki dai, Hukumar kula da harkar haƙa, saye da sayarwa na harkar man fetur da gas ta ƙasa NUPRC, ta kammal...
Daga Musa Muhammad
A halin da ake ciki dai, Hukumar kula da harkar haƙa, saye da sayarwa na harkar man fetur da gas ta ƙasa NUPRC, ta kammala shirye-shiryen kwashe wasu daga cikin sassan ma'aikatun ta daga Abuja zuwa Legas, kamar dai yadda Babban bankin Nijeriya da Hukimar kula da filayen jiragen sama suka yi.
Wannan shiri ya bayyana ne kamar yadda ya ke ƙunshe a cikin wata sanarwa mai ɗauke da kwanan watan 14 ga Fabrairu, 2024 wacce kuma Dokta Kelechi Onyekachi Ofoegbu ya sanya wa hannu.
Hukumar ta ce, an yanke shawarar ne a kan buƙatar inganta ayyukan Hukumar, rage kashe kuɗin aiki, da kuma yin amfani da kadarorin Hukumar da ke Legas.
Takardar ta ƙara da cewa, “Dangane da manufofin NUPRC na inganta ayyukan ta, haɓaka masana’antu da rage cunkuso a ofishin ta na Abuja, "muna duba yiwuwar mayar da wasu rukunai zuwa Legas", in ji sanarwar.
Ta ce, “Wannan yunƙurin ya samo asali ne daga buƙatar haɓaka ayyukan mu, rage kaahe kuɗin aiki, da yin amfani da isassun kadarorin mu da ke Legas.”
Wannan na zuwa ne makonni kaɗan bayan manyan rukunan Babban bankin Nijeriya, CBN da Hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta ƙasa (FAAN) sun mayar da ofisoshin su zuwa Legas saboda irin wannan dalili na inganta aikin.
Al'ummar yankin Arewacin ƙasar nan dai sun dage wajen sukar waɗannan matakai na gwamnatin Tinubu. Inda suka yi kukan cewa, a hankali, Tinubu na yunƙurin mayar da babban birnin tarayyar ƙasar nan daga Abuja zuwa Legas, wanda kuma ita gwamnatin ta musanta.
No comments