Wata kotun Shari'ar musulunci ta 1 da ke Unguwar GRA a Sabon Garin Zariya ta ƙwace wasu kadarorin Tsohon ɗan takarar Gwamnan jihar Kadun...
Wata kotun Shari'ar musulunci ta 1 da ke Unguwar GRA a Sabon Garin Zariya ta ƙwace wasu kadarorin Tsohon ɗan takarar Gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Muhammadu Sani Sha'aban, sakamakon bashin da wani Alhaji Umar Faruk Abdullahi ke bin shi.
A yayin yanke hukuncin, Mai Shari'a Alhaji Is'haq Madahu ya bayar da umirnin ƙwace ƙadarorin da aka sanya a matsayin garkuwa, a lokacin da aka yi yarjejeniyar karɓar bashin.
Bashin da Alhaji Umar Faruk Abdullahi ke bin Hon. Muhammadu Sani Sha'aban, su ne, Dalar Amurka $709, 238 da Naira Miliyan 11.2. Inda kuma nan take kotun ta bayar da izinin nemo masu sayen waɗannan kadarori na Hon. Sha'aban don a samu damar biyan wannan bashi.
Alƙali Madahu ya kuma bayyana cewa idan kuɗaɗen waɗannan kadarori sun zarce yawan kuɗin da ake bin Sha'aban, to za a mayar masa da abin da ya rage, haka kuma ba su kai kuɗin da ake bin sa ba, to shi kuma zai yi ciko.
Shi dai wannan bashi tsakanin Hon. Sani Mahmud Sha'aban da Alhaji Umar Faruk Abdullahi an sanya hannu a yarjejeniyar ne tun a shekarar 2018 don kuɗin da ya ke nema ya ceto kan sa daga wata matsala da ya shiga a Dubai a waccan shekarar.
Lauyan Hon. Sha'aban ne ya rubuta waccan yarjejeniyar, wanda kuma ya kasance cikin shaidun Sha'aban, tare da ɗan Sha'aban ɗin, sannan shi kuma Sha'aban ya sanya hannu bayan ya dawo.
An bi ƙa'idojin da Shari'ar musulunci ta gindaya wajen yarjejeniyar bayar da bashi, inda kuma aka sanya cewa za a kammala biyan bashin a tsakanin watannin shida.
Daga nan kuma sai a ranar 5 ga watan Disambar 2022, an kai ƙarar Hon. Sani Sha'aban, wanda ya nemi yin takarar Gwamnan jihar Kaduna a ƙarƙashin tutar Jam'iyyar APC, an kai ƙarar ne a Babbar kotun Shar'ar musulunci ta 1 da ke Zariya a kan ƙin biyan bashin Dalar Amurka Miliyan 1 da Naira Miliyan 11.200.
Mai ƙara, Umar-Faruk Abdullahi, ta hannun Lauyan sa, Usman Kuso ya roƙi kotun da ta bayar da umurnin sayar da Kadarorin wanda su ke ƙara game da bashin da su ke bi.
Lauyan ya zayyano Kadarorin da aka sanya a yarjejeniyar bashin, waɗanda kuma su ke so a sayar don su samu kuɗin su, akwai wani wuri a No.48 Yusuf road off Hadejiya road Bampai Kano a jihar Kano, wanda ke da shaidar mallaka mai lamba No.009234.
Sauran sun haɗa da katafaren ginin kamfanin Mazari Ltd da ke kan hanyar Kano zuwa Kaduna mai lambar mallakar C of O KD 6246, Zariya a jihar Kaduna. Akwai kuma wani na Tulips by MTD by Queen Elizabeth road GRA a Zariya ta jihar Kaduna.
“Haka kuma sauran suna haɗa da wani wuri a Circular road, GRA Zariya mai C of O no. KD11226. Akwai kuma wani da ke bayan babban gidan shi Hon. Sani Sha’aba ɗin da ke daura da makatantar Therbow Schools, GRA Zariya mai lambar C of O no. 3964” in ji Lauyan.
Haka kuma Lauya Kuso ya bayyana cewa cikin yarjejeniyar da aka rattaba wa hannu, an cimma matsayar cewa za a biya bashin Dala da Dala ne, sannan Naira da Naira.
Ya ce, tun lokacin da aka cimma wannan yarjejeniya a 2018, Sha'aban ya bayar da Dala 265,762 ne kawai a biya uku, inda mai bashin ya tsaya na tsawon shakara shida, amma ba a biya ba.
No comments