Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Akwai Alamun Shiga Matsalar Mai: Masu Tankar Man Fetur Sun Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki

Ga dukkan alamu za a shiga wani mawiyacin hali na ƙarancin man fetur da tarin layuka a gidajen mai a ƙasar, bisa barazanar shiga yajin aiki ...



Ga dukkan alamu za a shiga wani mawiyacin hali na ƙarancin man fetur da tarin layuka a gidajen mai a ƙasar, bisa barazanar shiga yajin aiki da ƙungiyar masu dakon mai ta 'Nigerian Association of Road Transport Owners,' inda su yi barazanar dakatar ɗaukar man. 

Ƙungiyar ta NARTO ta sha nuna damuwar ta bisa yadda man gas da suke zuba ma motocin nasu ya yi tsada, wanda kuma da waɗannan tankokin ne ake dakon man fetur zuwa sassan ƙasar nan. 

Suka ce farashin man gas na diesel ya fara ne daga N1,250 zuwa N1,400 a kowace lita ɗaya, farashin ya danganta ne da inda aka saya. 

A ciki wata sanarwa, Shugaban ƙungiyar ta NARTO, Yusuf Othman ya fitar a Abuja, ya bayyana cewa wannan bayani tamkar wata matsaya ce ta uwar ƙungiyar daga hedikwatar ta, cewa mambobin nasu za su ajiye tankokin su daga ranar Litini. 

 Ya ce wannan mataki nasu ya zama wajibi, bisa la'akari da irin asarar da suke tafkawa a harkar jigilar man, kuma ba za su iya jure wannan asarar ba. 

NATO ta ce, “Za mu dakatar da aiki daga yanzu zuwa Litini. Ba za mu iya aiki cikin asara ba, yawancin mu duk mun ajiye motocin mu, wasu kuma nan za su bi sahu."

Shugaban ya ce sun rubuta takardar koke ga shugaban ma'aikatan ofishin shugaban ƙasa, Ministan man fetur, Hukumar tsaro da DSS da sauran masu ruwa da tsaki a harkar man, amma babu wata natija da aka samu.

Wakilin Matattarar Labarai ya labarto mana cewa yanzu haka an fara dogayen layuka gidajen mai a Abuja, a Kaduna ma, wasu gidajen man, musamman a kan bypass, duk sun kulle, wai babu mai.

No comments