Nan da 'yan makwanni kaɗan ne za mu shiga watan Azumin Ramadan, inda a ciki ake nunnunka lada ga kowace ibada. Amma ganin yadda wasu Lim...
Nan da 'yan makwanni kaɗan ne za mu shiga watan Azumin Ramadan, inda a ciki ake nunnunka lada ga kowace ibada. Amma ganin yadda wasu Limamai da Malamai ke wuce ƙa'ida wajen gudanar jagorancin ibada a masallatansu, Hukumomi a ƙasar Saudi Arebiya sun gindaya wasu ƙa'idoji da za a bi a cikin watan.
Ganin cewa kowane ɗan adam akwai mataki na imanin sa, wanda kuma bai kamata wani ya cutar da wani wajen gudanar da masa ba, abubuwan da aka haramta sun haɗa da cewa za a kashe lasifika lokacin sallar asham. Sannan an hana yaɗa bidiyon sallar asham da ta tahajjudi a kafafen yaɗa labarai a duk faɗin duniya.
Haka kuma Hukumomin na Sadiyya sun haramtawa masu yin i’itikafi a masallaci har sai an tantance mutum. An kuma sanya dokar taƙaita sallar dare da ake yi lokacin azumi don kowa ya koma gida da wuri.
Sannan kuma Hukumar ta haramta neman taimako ko tallafi a harabar masallaci da wasu ke yi don bada buɗa baki. An kuma hana iyaye zuwa masallaci da yara, inda aka buƙaci masu yara su bar su a gida.
Cikin abubuwan da ba za a sake yarda da shi ba, shi ne yin buɗa baki a farfajiyar masallacin Makka da Madina. An luma bada umarnin kashe lasifika ko Kuma rage sautinta.
Kamar dai kowace doka, wannan mataki na Hukumomin Sadiyyar dai bai yi wasu daɗi ba, yayin da wasu kuma ke murna da umurnin.
No comments