Daga Ibrahim Muhammad Kano A kwanakin baya ne al'ummar Kawaji da ke jihar Kano suka yi taron taya murna ga Dagacin yankin, Alhaji Musa A...
Daga Ibrahim Muhammad Kano
A kwanakin baya ne al'ummar Kawaji da ke jihar Kano suka yi taron taya murna ga Dagacin yankin, Alhaji Musa Adamu akan cikar sa shekaru 50 akan karagar mulki.
Da yake zantawa da 'yan jarida a fadar sa, Dagacin ya ce waɗannan Shekaru ya yi su ne cikin nasara da kawo ci gaba mai yawa, don haka duk abin da Mutum ya sa a gaba ya kamanta gaskiya shi ne zai kawo ci gaba da ƙauna ga waɗanda ake jagoranta.
Ya ce, Dagacin ya ce ya zauna lafiya da mutane, an kawo makarantu da Asibitoci a lokacin sa, da tsayawa don sanya yara a makarantu su yi ilimi da ba su da adadi.
Ya ce, duk da raba sarauta da ayyukan gudanarwa na al'umma da aka yi, har yanzu jama'a ba ta rabu da su ba.Ita kanta Gwamnati tana neman gudummawar su in wani abu ya sha kanta domin har yanzu masarauta na tare da mutane.
Dagacin na Kawaji Alhaji Umar Adamu ya yi kira ga al'umma akan su rungumi zamani sai su zauna lafiya, duk abin da Allah ya kawo idan mai amfani ne su riƙe shi, "amma in ka ce ba za ka yi hakan ba, to za a tafi a bar ka ne. Duk abin da ake idan ba zai kai ka ga faɗawa haɗari ba ne, ka rungume shi, sai a tafi da kai."
Ya ce, yana godiya ga al'ummar Kawaji bisa haɗin kai da suka ba shi, kuma ko da taron jama'a ne suka yi kaiwa da kawowa saboda ƙauna. Ya kuma gode wa Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda Mai Gidan sa ne tun yana Hakimi a Nasarawa, shi ya zama wakilinsa .
Shi ma Mai Unguwar Kawaji cikin gari, Alhaji Auwalu Umar, wanda ya ke babban ɗa ne ga Dagacin, kuma ɗaya ne daga Wanda suka tsara taron, ya ce kusan wata ɗaya suna tsara yadda za a yi a taron da aka yi aka gama lafiya, sun gayyaci mutane da dama, kuma sun halarta wasu sun turo wakilai da fatan alkhairi.
Ya ce sun sami ƙwarin gwiwar yin taron ne duba da yadda Allah cikin ikon sa in ya so ka daɗe, sai ka jima a raye a haifi wani ma bai shekara ba ya mutu, amma mahaifinsu tun suna yara ƙanana suka je wajen naɗa shi.
Ya ce mahaifin nasu Dagacin Kawaji cikin ikon Allah wannan a tsawon lokaci na shekara 50 da naɗa shi, Unguwanni 18 da ke ƙarƙashin sa ba inda aka taɓa kuka da shi, ba wani abu da zai taso bai je ba, ko ya tura wakilci.
Ya ce rayuwar mahaifin su ta zame musu tamkar makaranta, suna ganin abubuwa da yake na arziki suna sawa a ƙwaƙwalwarsu yana zame musu abin dubawa na gyara ɗabi'ar su domin ya san mu'amala mai kyau da mutane na zaman lafiya.
Alhaji Awwal Umar Adamu ya ce abin da ya jawo wa Mahaifin su jama'a shi ne irin tawali'un sa da rashin girman kai, kowane irin Mutum ne zai saurare shi ya sami tarbiyya tun daga Marigayi Sarkin Kano Ado Bayero.
No comments