Ƙungiyar Masu Dakon Man Fetur ta Nijeriya (NARTO) ta sanar da janye yajin aikin gama-gari da ta soma a ranar Litinin. Tuni dai shugaban Ƙung...
Ƙungiyar Masu Dakon Man Fetur ta Nijeriya (NARTO) ta sanar da janye yajin aikin gama-gari da ta soma a ranar Litinin.
Tuni dai shugaban Ƙungiyar NARTO na ƙasa, Othman Yusuf, ya umarci mambobinsu da su dawo bakin aiki nan take a fadin kasar.
Matakin hakan na zuwa ne bayan shiga tsakani da Gwamnatin Tarayya da sauran masu ruwa da tsaki a fannin albarkatun man fetur suka yi kamar hukukomin da ke kula da dokokin man fetur irinsu NNPCL, NMDPRA, DAPPMA da dai sauran su.
A jawabin sa ga manema labarai bayan wata ganawar sulhu da ta gudana tun daga ranar Litinin zuwa maraicen Talata, Ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur, Ekperipe Ekpo, ya ce ƙungiyar NARTO ta dakatar da yajin aikin gama-gari da ta shirya daga jiya litinin 19 ga watan Fabrairun shekarar 2024 da muke ciki.
An ruwaito cewa, mambobin kungiyar NARTO dai sun dakatar da ayyukansu na jigilar man fetur a fadin kasar sakamakon tsadar man dizal da kuma matsin tattalin arziki a kasar.
Mambobin kungiyar NARTO sun yi barazanar tsayar da ayyukansu a fadin kasar tun daga jiya Litinin saboda tsadar man dizal wanda ake amfani da shi wajen jigilar man fetur da motocinsu a fadin Nijeriya.
Kamar man fetur wanda a yanzu ake sayar da shi daga kan Naira dari 6 zuwa 7 kan kowace lita, farashin man dizal ya yi tashin gwauron zabi a musamman a baya-bayan nan, lamarin da ba ya rasa nasaba da tashin farashin dala a kasuwannin bayan fagge da na hukuma a kasar.
A yanzu dai ana sayar da man dizal sama da Naira dubu 1 da 250 duk lita a Nijeriya.
No comments