Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yawan Haddasa Haɗurra Na KASTLEA Kaduna: Kwamishina Ya Kira Taron Masu Ruwa Da Tsaki

Daga Musa Muhammad, Kaduna Ganin irin haɗurran da jami'an kula da tilasta bin ƙa'idojin hanya ta jihar Kaduna KASTLEA suke haddasawa...

Daga Musa Muhammad, Kaduna

Ganin irin haɗurran da jami'an kula da tilasta bin ƙa'idojin hanya ta jihar Kaduna KASTLEA suke haddasawa a titunan jihar, Kwamishinan mai'aikatar ayyuka, Dr Ibrahim Hamza ya kira wani taro na masu ruwa da tsaki a harkar sufuri, tare da jami'an Hukumar don lalubo hanyoyin da za a magnace matsalar. 

Kwamishinan ya ce, samun daidato da tafiya kafaɗa da kafaɗa tsakanin jami'an KASTLEAr da masu harkar sufuri zai matuƙar taimakawa wajen samun fahimtar juna da bin doka da oda. 

Ya ce, "Saboda haka ne muka ga ya wajaba mu kira wannan taro a yau don samun hanyoyin tattaunawa da ji daga juna, har a samu hanyoyin da za a samu kariya da abin doka da oda a hanyoyin mu. 

"Don haka, ya na da muhimmanci mu sani cewa kiyaye ƙa'idoji da dokokin hanya don samun tsirar kowa ne a hanyoyi, kuma abu ne da ya hau kan kowa, duk mai bin hanya.'

Kwamishinan, wanda babban Sakatare a ma'aikatar, Alhaji Abdu Na Abdu Ashiru ya wakilta, ya bayyana wasu halaye da jami'an kula da bin dokoki hanyar ke aikatawa, waɗanda kuma sun saɓa da damar da tsarin mulki ya ba su. 

Ya ce, irin waɗannan halayen ne a yawanci  lokuta ke haddasa tashin-tashina tsakanin jami'an kula da bin dokar hanyar da kuma Direbobi.  

Don haka ne Dr. Ibrahim Hamza ya ƙara jaddada cewa, wannan ne babban dalilin da ya sa aka kira wannan taron, don a samar da wata dama da za a saurari ɓangarorin biyu, inda ake son kowa ya fito fili ya yi bayanin matsalolin sa, ba tare da wani ɓoye-ɓoye ba. Magana ake so ta gaskiya, don samun hanyar tabbatar da tsaro a hanyoyin mu. 

Ya ce, za a iya kaucewa tare da rage yawan haɗurra a hanyoyin mu, ta hanyar bin ƙa'idojin da aka tanada, musamman gudun da ya wuce misali. 

Tun farko a cikin jawabin ta, shugabar Hukumar KASTLEA, Mrs Carla Abdulmalik ta bayyana wannan taro na masu ruwa da tsaki a harkar sufurin a matsayin dama da za a ilimantar game da sanin ƙa'idoji da dokokin hanya. 

Ta kuma nuna damuwar ta bisa yadda manyan motoci ke yawan rufe hanyoyin jihar kan ɗan abin da bai taka kara ya karya ba. 

Daga nan Mrs Abdulmalik ta nemi masu ruwa da tsaki a harkar sufurin, da ma sauran matafiya masu bi ta jihar, su tabbatar sun yi tuƙi da kula, tare da bin dokokin da aka tanada. Haka kuma ta musanta batun da Direbobin ke yi na tsawwala tarar masu laifi.

Da ya ke tofa albarkacin bakin sa, Shugaban Ƙungiyar masu motocin haya ta jihar Kaduna NARTO, Alhaji Sa’idu Mustapha Basawa ya yi zargi jami'an kare dokokin hanyar da cewa ba sa aiki bisa dokar da ta kafa su, wanda hakan ya sa su ke yawan haddasa matsaloli da cunkoso a hanyoyi.

A ƙarshe, Alhaji Sa'idu Basawa ya roƙi gwamnati ta gyara manya da ƙananan hanyoyin jihar don a rage matsalolin da ake fuskanta.

Jama'a a mazauna jihar Kaduna, da ma masu bi ta jihar su wuce, musamman direbobi sun jima suna kokawa game da yadda jami'an na KASTLEA ke ci masu mutunci, musamman idan direbobin sun ƙi yarda su ba su cin hanci. 

Yawancin direbobin da Matattarar Labarai ta zanta da su, sun nuna matuƙar dumuwar su game da ayyukan waɗannan jami'ai, waɗanda suka ce suna ƙetare haddi a bakin aiki,  musamman karɓar cin hanci, wanda in an ba ƙi ba su, sai su ci zarafin direba. 

 

No comments