Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ku Zama Alami Na Ƙarfafa Gwiwar Marasa Ƙarfi - Gwamnan Zamfara Ga Sabbin Alƙalan Musulunci

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ƙalubalanci Sabbin Alƙalan Kotunan Shari'ar musulunci su uku da aka rantsar yau Laraba, kan su kas...

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ƙalubalanci Sabbin Alƙalan Kotunan Shari'ar musulunci su uku da aka rantsar yau Laraba, kan su kasance masu tsare gaskiya a yayin gudanar da ayyukan su, inda kuma ya yi kira gare su da su zama alami na ƙarfafa gwiwar marasa ƙarfi. 

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa kotunan Shari'a na bayar da Gagarumar gudumawa wajen inganta harkar Shari'a ta jihar. 

Ya ƙara da cewa, an ƙara faɗaɗa kotunan Shari'a a Zamfara ne a shekarar 1999 don su kula da manyan laifuffuka da makamantan su, wanda ke sahun gaba wajen tabbatar da adalci. 

Haka kuma a cikin jawabinsa wajen wannan bikin rantsarwar, kar yadda ya ke ƙunshe a cikin sanarwar ta Sulaiman Bala, Gwamna Dauda Lawal ya hori sabbin Alƙalan da su tabbatar sun kare mutuncin aikin nasu.  

Gwamnan ya ce, “Na tabbatar da cewa zaɓo ku da aka yi don ku zama Alƙalan kotunan ɗaukaka ƙara na Shari'ar musulunci bai rasa nasaba da kasancewar ku masana ilimin Shari'ar musulunci, waɗanda suka daɗe a kan aikin, sannan kuma suka jajirce wajen kare martabar Shari'ar. 

“Kuna da gagarumar gudumawar da za ku bayar wajen yi wa jama'a adalci. Na ku kawai, shi ne tsare gaskiya. A matsayin ku na Alƙalai, yana da muhimmanci ku san da cewa za ku tsaya gaban Allah a gobe Ƙiyama don yin bayanin abin da ku ka aikata. 

Daga nan Gwamnan ya hore su da su tabbatar da sun riƙe amincin da jama'a ke da shi ga tsarin Shari'ar musulunci, su jajirce da ganin cewa kotunan su sun tabbata wurin samun wata fata ta adalci ga jama'a, musamman marasa ƙarfi. 

“A tsarin mu na ceto jihar Zamfara, ina tabbatar maku da cewa gwamnati na a shirye ta ke wajen aiwatar da Shari'ar musulunci a duk faɗin jihar, a fannin shari'o'i da aiwayar da ayyuka. 

“Daga wannan rantsarwa ta yau, ku sani cewa kuna da babban aiki a gaban ku wajen kare martabar Shari'a. Wajibi ne a yi wa kowa adalci, ba tare da la'akari da siyasa, arziƙi ko matsayin mutum ba, " in ji Gwamnan. 

 

No comments