Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mutune 23 A Abuja

A daren Asabar ne ’yan bindiga suka yi awon gaba da wasu mutane ashirin da uku a unguwar Dei-Dei da ke ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Bwari a bab...



A daren Asabar ne ’yan bindiga suka yi awon gaba da wasu mutane ashirin da uku a unguwar Dei-Dei da ke ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Bwari a babban birnin tarayya.

An samu labarin cewa an ɗauke waɗanda abin ya shafa ne daga gidajensu da rukuni ɗaya, tsakanin ƙarfe 8 zuwa 9 na safe.

Mai Unguwar Dei-Dei Ibrahim Galadima yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a daren jiya, ya ce jami’an tsaron da ke yankin sun ceto bakwai daga cikin waɗanda abin ya shafa, inda suka bi sahun masu garkuwa da mutane cikin daji bayan kimanin sa’a guda.

Ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Abuja ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

No comments