Jakadan Falastinu a Nijeriya, Abu Shawesh ya bayyana cewa, idan ta'asar da Isra'ila ke yi a Gaza ba kisan ƙare dangi ba ne, a bayyan...
Jakadan Falastinu a Nijeriya, Abu Shawesh ya bayyana cewa, idan ta'asar da Isra'ila ke yi a Gaza ba kisan ƙare dangi ba ne, a bayyana sabon ma'anar kisan ƙare dangi.
Ambasada Shawesh ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da ya fitar kwanan nan.
Ya ce, "A safiyar ranar 1 ga watan Disamba ne dai sojojin Isra'ila suka cigaba da kai hare-hare bayan shafe kwanaki 7 ana kai hare-hare. Babu lokacin makoki a Gaza, sai dai lokaci da za a jira mutuwa, a ƙirga waɗanda aka kashe, a kuma yi hasashen waɗanda za a kashe a gaba. Palastinawa dai sun rasa fata kwata-kwata; kuma sun tabbata cewa duniya ta juya masu baya, ta bar su a bakin shaiɗaniyar kada (Isra'ila).
"Bayan 'yan kwanaki na tsagaita buɗe wuta na jinƙai, ƙishirwar jinin Falastinawa da Isra'ila ta yi ya sa ta yi gaggawar cigaba da wani sabon zagaye na kisa. Dattin hannaye da yatsu na matuƙan jirage masu aikata laifuka sun cigaba da zubar da jinane a yaƙin."
Sanarwar ta ƙara da cewa, "Abin baƙin ciki shi ne, dole ne in sake yin magana game da batu mai ban tausayi da muhimmanci wanda zan gwammace kada in tattauna alkaluman masu raɗaɗi. A ranar 62 na littafin Kisan Ƙare Dangi, adadin waɗanda suka mutu ya zarce 17,000 da suka haɗa da yara 7,224 da mata 5,818, tsofaffi 478, ma’aikatan kiwon lafiya 281, 'yan jarida 77, 46,000 suka jikkata, a bayyane yake cewa yawancin waɗanda abin ya shafa yara ne da mata. Rukunan gidaje 43,000 sun lalace gabaɗaya sannan wasu 255,000 sun lalace sosai, mutane miliyan 1.9, kwatankwacin kashi 80% na al'ummar Gaza, sun zama 'yan gudun hijira da ƙarfi."
"A Yammacin Kogin Jordan, tun ranar 7 ga Oktoba, Sojojin Haramtacciyar ƙasar Isra'ila sun kashe Falastinawa 243, ciki har da yara 65."
"A ranar 28 ga Nuwamba, ranar sulhu, likitocin sun sami damar komawa cibiyar kula da lafiya ta Al Nasr da ke Gaza, inda daga baya aka tilasta kwashe su a ranar 10 ga Nuwamba, inda suka bar jarirai. Bayan dawowarsu, sun tarar da jarirai 5 sun mutu. Hotunan bidiyo da dama da aka yada a kafafen sada zumunta daban-daban sun nuna yadda jikinsu ya ruɓe," inji sanarwar.
"Wani lamari mai matuƙar muhimmanci wanda bai shiga labaran duniya ba. Tun bayan sabon harin da Isra'ila ta kai a yankin West Bank, mutum 3,640 ne aka kashe, ciki har da yara 245, mata 147, 'yan jarida 41, da fursunonin gudanarwa 1,666. Fursunoni 7 ne suka yi shahada a gidajen yarin Isra'ila: Omar Daraghmeh daga Tubasz Arafat Hamdan fiom Ramallah, Majid Zaqqui daga Gaza, Abdulrahman Maree daga Salfit da Thaer Abu Asab daga Qalqilia sun mutu sakamakon tsananin duka da azabtarwa, da wasu mutane biyu da ba a san sunayensu ba."
"Bayan kama su, Sojojin Isra’ila (IOF) sun kutsa cikin gidajensu, suka yi musu mugun duka a gaban iyalansu, suna zaginsu, suna yi musu barazana, sun yi biris da raunin da suka ji da kuma yanayin lafiyarsu.
"Hukumar kula da gidajen yari ta Isra'ila ta ɗau matakan ladabtarwa da dama a kan fursunonin, wanda ya zo daidai da dokar hana bayanai gabaɗaya domin ɓoye laifukan da aka aikata a kansu."
Sanarwar ta ci gaba da cewa, "wannan ya haɗa da hana kai ziyara na ‘yan uwa da lauyoyi, da kuma kai hare-hare a kullum a dakunan fursunonin a lokacin da sojoji suka yi wa fursunonin mumunar duka ta hanyar amfani da sanduna, bindigu, gas, da harsashin roba, wanda hakan ya sa su samu raunuka masu zurfi, da karaya a hannuwa da kafafun su. Abincin da aka tanadar yana musu abun ƙyama ns, an tsara shi don barin su da yunwa ne datse musu rayuwa. A ɗakuna kwana kuwa, akwai matuƙar cunkoson jama’a kuma ba su da isassun gadaje, barguna, da sauran kaya.
"Wannan yana hade da rashin kasancewar kungiyar agaji ta Red Cross da sauran kungiyoyin kare hakkin bil adama da ya kamata su sanya ido da bayar da rahoto kan wannan lamarin. Yana da kyau a lura cewa hatta gawarwakin fursunonin da suka mutu ana amfani da su wajen makamashi, kamar yadda aka gani a misalan baya-bayan nan.
"Nasser Abu Hmid, wanda ya mutu sakamakon rashin kula da lafiya, da kuma Adnan Khader wanda aka tsare ba tare da bin sawu ba, ya kuma tafi yajin cin abinci har ya mutu.
"Da wannan magana, shin na tona wani sirri ne a lokacin da na ce da yawa daga cikin ƙasashen yammacin duniya suna da hannu dumu-dumu a cikin kisan gilla ga al'ummar Palastinu? Ko kuwa na tona asiri ne a lokacin da na ce hannayensu sun ɓaci da jinanen yaran Falastinu?
"Ana buƙatar shiru ne a lokacin da yaran ke kan gadon barcin su, ba lokacin da ake kashe su ba.
"Ta'addancin ƙasa shi ne mafi munin ta'addanci. Isra'ila ita ce cikakkiyar ma'anar ta'addancin ƙasa.'
No comments