Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yadda Magidanci A Bauchi Ya Yi Wa Matarsa Fashi, Bayan Ya Sumar Da Ita

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Bauchi ta cafke wani magidanci kan yunƙurin kashe matarsa lokacin da ya je yi mata fashi cikin hijabi a gidan...

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Bauchi ta cafke wani magidanci kan yunƙurin kashe matarsa lokacin da ya je yi mata fashi cikin hijabi a gidansu na aure, tare da yi mata barazana da taɓarya.

Kwamishinan 'yan sandan Bauchi, CP Auwal Musa Mohammed ya ba da umarnin cewa a mayar da maganar zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar don bankaɗo haƙiƙanin abin da ya faru tsakanin magidancin da ake zargi da mai ɗakinsa.

Wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, SP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar a ƙarshen mako ta ce tuni jami'ansu suka kama magidancin mai shekara 35 da haihuwa.

Sanarwar ta ce, "ana zargin magidancin wanda muka sakaya sunansa da kai wa matarsa farmaki da haddasa mugun rauni da yunƙurin aikata laifin da ya yi daidai da kisan kai".

Ahmed Wakil ya ce, a ranar Asabar 2 ga watan Disamba ne suka samu rahoton faruwar wannan lamari, inda suka garzaya wurin da abin ya faru tare da ɗaukan matar da aka yi wa fashi zuwa asibitin ƙwararru na jihar Bauchi.

'Yan sanda sun ce, binciken farko-farko sun bayyana cewa, mutumin da ake zargi ba tare da yawan turjiya ba, ya amsa cewa ya aikata abin da ake zarginsa da shi.

"A jawabinsa, wanda ake zargi ya ankarar da matarsa bisa ƙarya cewa 'yan fashi sun shiga gidansu, kuma cikin hanzari ya shiga ɗakinta ya ce ta rufe fuskarta da hijabi.

"Daga nan sai ya fito daga ɗakin, ya rufe fuskarsa da hijabi, tare da ɗaukar taɓarya sannan ya koma ɗakin, inda ya fara buga wa matar taɓaryar," inji sanarwar 'yan sanda.

'Yan sanda sun ce wanda ake zargi ya ƙara shaida musu cewa ya yi niyyar halaka matar tasa tare da ɗauke talbijin ɗinta don sayarwa ya ƙara jarin shagonsa.

SP Ahmed Wakil ya ce, za su gurfanar da magidancin da ake zargi a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.

No comments