Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziki zagon ƙasa da sauran ayyukan zambar kuɗi ta EFCC ta gurfanar da wata mata mai suna Aisha Salihu Malk...
Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziki zagon ƙasa da sauran ayyukan zambar kuɗi ta EFCC ta gurfanar da wata mata mai suna Aisha Salihu Malkohi (wacce ake ma laƙabi da Ummitah, Arab Money), tare da mijinta, Abubakar Sadiq Mahmoud, wanda kuma yanzu haka ya gudu, bisa zargin zambar tsabar kuɗi har (Naira Miliyan Ɗari Huɗu da Goma da Ɗubu Ɗari Biyar da sha Takwas ) N410,518,000.
A cikin wata sanarwa da Hukumar ta wallafa a shafin ta na tweeter, ta bayyana cewa an gurfanar da mijin da matar ne ranar Juma'ar da ta gabata a gaban Mai Shari'a Aisha Mahmud ta babbar kotun jiha da ke Kano.
Hukumar ta ci gaba da cewa, ɗaya daga cikin laifukan da ake tuhumar waɗannan ma'aurata, duk da dai mijin ba ya kotun, domin ya gudu, shi ne "Ke Aisha Salihu Malkohi da Abubakar Sadiq Mahmoud, a tsakanin shekarar 2022 a Kano ta jihar Kano, wanda kuma wannan kotu ke a wannan yankin, kun karɓi kuɗi N225,259,000 daga Farida Ibrahim a tsakanin 6 ga Janairu zuwa 16 ga Disambar 2022 a wani asusun banki mai ɗauke da sunan Abubakar Sadiq Mahmoud a bankin Zenith, wanda kuma kun karɓi kuɗin ne don sayo wasu motoci guda 64 daga ƙasar Saudi Arebiya, wanda kuma ku na sane cewa ƙarya ce. Don haka kun saɓa dokar sashe na 1 (a)&(b) hukunci ƙarƙashin sashe na 1 (3)".
Sai dai ita Aisha Salihu ta ƙi amimcewa da duk waɗannan tuhume-tuhume da aka yi masu.
Don haka, sakamakon roƙon da ta yi, Lauyan Hukumar ta EFCC, Zarami Mohammed ya nemi kotun ta sanya ranar da za a fara sauraren Shari'ar.
Lauyan waɗanda ake tuhuma, G.I Abubakar ya nemi kotun da ta bayar da belin waɗanda ya ke karewa, amma Lauyan EFCC ya soki wannan buƙata.
Daga nan kuma sai Mai Shari'a Aisha Mahmud ta ɗage sauraron ƙarar zuwa 15 ga wannan wata na Disamba don yanke hukunci game da belin da aka nema. Mai Shari'ar ta kuma ba da umurnin a ci gaba da tsare wacce ake tuhuma a hannun EFCC har zuwa ranar.
Jami'an bincike na musamman na Hukumar EFCC ɗin ne suka damƙe Aisha Malkohi a Kano, sakamakon koken da wasu mutum biyu, Farida Ibrahim da Ibrahim Mohammed Abdulrahman suka shigar gaban ta, bisa zargin cewa Aisha ta haɗa baki da mijin ta, inda suka zambacewa maƙudan kuɗaɗen da suka tara da gumin su, da sunan za a sayo masu motoci, gwala-gwalai, kaya masu aiki da lantarki da kuma kayan kicin daga Saudiyya.
Hukumar ta ce, tana karɓar wannan koke sai ta tsunduma cikin bincike, inda ya zuwa yanzu ta gano cewa waɗannan mutane sun karɓi kuɗi N410,518,000 ta asusun kamfanin matar, wato 'Golden Grass Hill International Ltd,' tare da asusun bankin mijin da ke bankin Zenith.
Hukumar ta ce, sannan kuma bincike ya nuna cewa matar da mijin na ta, wanda yanzu haka ya tsere, sun rarraba waɗanda kuɗaɗe zuwa ma'ajiyoyi na bankuna daban-daban.
No comments