Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Majalisar Dattawa Ta Sadaukar Da Albashinta Na Disamba Ga Al'ummar Tudun Biri

Majalisar Dattawa ta 10 ta bayar da gudunmuwar Naira Miliyan 109 ga waɗanda harin bam ɗin sojoji ya shafa a ƙauyen Tudun Biri da ke Ƙaramar ...



Majalisar Dattawa ta 10 ta bayar da gudunmuwar Naira Miliyan 109 ga waɗanda harin bam ɗin sojoji ya shafa a ƙauyen Tudun Biri da ke Ƙaramar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, wanda ya sanar da bayar da tallafin a lokacin da ya jagoranci wasu manyan Hafsoshi da Sanatoci a ziyarar ta’aziyyar da suka kai wa Gwamna Uba Sani a gidan gwamnatin Sir Kashim Ibrahim a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce tallafin na jin daɗin waɗanda abin ya shafa ne, wanda ya kasance albashinsu na Disamba.

Yayin da yake jajanta wa gwamnatin jihar Kaduna da al’ummar yankin Tudun Biri kan wannan mummunan lamari, mataimakin shugaban majalisar dattijai, wanda ya wakilci shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio, ya ce majalisar za ta haɗa kai da fadar shugaban ƙasa domin bankaɗo al’amuran da suka dabaibaye majalisar na harin bam na ba-zata akan fararen hula da ba su ji ba, ba su gani ba a ƙauyen Tudun Biri domin kauce wa sake afkuwar lamarin.

A nasa ɓangaren, Gwamna Sani ya gode wa Sanatocin bisa yadda suka nuna juyayi ga waɗanda harin ya shafa, don haka ya yi kira ga Majalisar Dokoki ta kasa da ta goyi bayan Gwamnatin Tarayya wajen gudanar da bincike kan lamarin.

Ya kuma yi kira ga ‘yan majalisar tarayya da su sake duba batun samar da ‘yan sandan jihohi. Ya ce hakan zai ƙarfafa harkokin tsaro a ƙasar.

No comments