Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Bam A Tudun Biri: A Biya Diyyar Waɗanda Suka Rasa Rayukan Su -Wazirin Santuraki

  Daga Imrana Abdullahi Shugaban Majalisar ƙolin Ƙungiyar masu Noman Zamani ta ƙasa, Alhaji Dokta Aliyu Muhammad Waziri, Santurakin Tudun Wa...

 

Daga Imrana Abdullahi

Shugaban Majalisar ƙolin Ƙungiyar masu Noman Zamani ta ƙasa, Alhaji Dokta Aliyu Muhammad Waziri, Santurakin Tudun Wada Kaduna, Khadimul Islam ya yi Kira ga Gwamnatin tarayyar Najeriya da ta biya diyyar waɗanda suka mutu, tare da ɗaukar nauyin waɗanda suka samu rauni ko jikkata a sakamakon harin Bam ɗin da aka kai wa masu Maulidin Annabi a ƙauyen Tudun Biri da ke Ƙaramar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.

Santurakin Tudun wada Kaduna, wanda ake yi wa laƙabi da Ɗan Marayan Zaki, Alhaji Dokta Aliyu Muhammad Waziri ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya kira a garin Kaduna. 

Ya ci gaba da cewa, "Kuma kamar yadda rundunar soja ta tabbatar cewa kuskure ne, don haka lallai a biya diyya kuma a ɗauki nauyin maganin waɗanda suka ji rauni a sakamakon harin.

"Muna kuma yin kira da babbar murya ga Gwamnatin tarayya da ta gudanar da bincike game da wannan lamari na harin bam da aka yi a ƙauyen Tudun Biri."

Aliyu Waziri ya kuma jinjina wa shugaban Ƙasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu bisa irin kyawawan tsare-tsaren da yake yi wa aikin Noma da kuma gabatar da tsarin wadatar da ƙasa da abinci da nufin samun abubuwan da ya dace a ƙasa har ma da ƙasashen ƙetare.

A ƙarshe ya yi addu'ar Allah ya tona asirin duk waɗanda ke haifar da fitinar da za ta haifar da tashin-tashina a duk faɗin Najeriya.

No comments