Daga Hussaini Yero Sabon Magajin garin Funtuwa na biyar, Alhaji Shehu Nuhu ya samu Kyakkwar tarba tun daga fadar mai Martaba Sarkin Katsina,...
Daga Hussaini Yero
Sabon Magajin garin Funtuwa na biyar, Alhaji Shehu Nuhu ya samu Kyakkwar tarba tun daga fadar mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abudulmumini Kabir, har zuwa Ƙarama Hukumar Funtuwa inda ya ke da fadarsa.
A jerin Magajin garin Funtuwa, waÉ—anda suka hau karagar mulkin na Magajin gari, su ne: Magajin Gari Dabo, sai na biyu Magajin Gari Nuhu, sai na uku Magajin Gari Ali, sai na huÉ—u, Magajin Gari Rabiu, sai na biyar sabon Magajin gari Shehu, Wanda a ranar Asabar 9/12/2023 ne Mai Martaba Sarkin Katsina ya naÉ—a shi, a fadar sa da ke Katsina.
A jawabin sa, Sabon Magajin garin na Funtuwa, Alhaji Shehu Nuhu ya yi ma Allah godiya akan wannan sarauta da ya samu. Ya kuma miƙa godiyar sa ga 'yan uwan sa na jini da suka tsaya tsayin-daka don ganin ya gaji wannan kujerar ta iyaye da kakani. Ya kuma gode ma abokan arziki da auransu .
Magajin Shehu ya tabbatar da cewa yana da tsare-tsare na musamman don ci gaban garin Funtuwa.
No comments