Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Zamfara Ta Kammala Kashi Na Biyu Na Shirin Kula Da Lafiya Kyauta Ga Jama'a

Gwamnatin Jihar Zamfara ta kammala kashi na biyu na shirin kula da lafiyar jama'a kyauta, musamman mutanen karkara.   Kashi na farko na ...



Gwamnatin Jihar Zamfara ta kammala kashi na biyu na shirin kula da lafiyar jama'a kyauta, musamman mutanen karkara.
 
Kashi na farko na Shirin na Musamman na Fannin Kiwon Lafiya ya fara ne a cikin watan Agusta, inda aka bayar da kulawa na kiwon lafiya kyauta ga mutanen da ke da matsalar ido, kumburin hanji kamar 'hernias da hydroceles', kula da masu yoyon fitsari, da ilimin kiwon lafiya.
 
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa an samu nasarar kula da lafiyar mutane 1,858 a matakin farko da na biyu.
 
A cewarsa, kashi na biyu ya kasance daga ƙarshen watan Nuwamba zuwa makon farko na watan Disamba.
 
Ya ce, “Gwamna Dauda Lawal ne ya fara gudanar da gyare-gyaren aikin jinya da ake cigaba da yi don ƙauracewa yawan tiyata a Zamfara, da suka haɗa da matsalar ido, kumburin hanji (hernias, hydroceles), yoyon fitsari (VVF), da kuma ilimin kiwon lafiya.
 
“Shirin na musamman wanda Farfesa A. I. Mungadi ya jagoranta tare da kwararrun likitoci, ya samu gagarumar nasara wajen yin aiki a kan matsaloli kiwon lafiya 1,858.

“Shirin yana amfani wajen bayar da kulawar kwararru ta musamman ga majinyata daga ƙauyuka da ƙananan birane, wanda ya shafi ƙananan hukumomin jihar 14, wannan tsarin ya baiwa marasa lafiya da ke wurare masu nisa samun kulawar ƙwararru likitocin da suke buƙata.
 
“Da wannan shiri, gwamnatin jihar Zamfara na da burin inganta lafiyar jama’a da jin daɗin jama’a, rage yawan mace-mace, da samar da ingantacciyar lafiya ga al’umma.”

No comments