Ministan Ma’adinai, Mista Dele Alake, a ranar Talata, ya yi zargin cewa wasu manyan ƙusoshin ’yan Nijeriya da ke da hannu wajen haƙar ma’ada...
Ministan Ma’adinai, Mista Dele Alake, a ranar Talata, ya yi zargin cewa wasu manyan ƙusoshin ’yan Nijeriya da ke da hannu wajen haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba suna ɗaukar nauyin ’yan fashin daji da ta’addanci a ƙasar.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai kan ma’adanai masu ƙarfi don kare kasafin kudin ma’aikatar na 2024 a Abuja, babban birnin ƙasar.
Alake ya kuma yi zargin cewa suma ‘yanasashen waje suna haƙo ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a lasar. Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta mai da hankali sosai kan harƙar hakar ma’adinai da za ta riƙa karɓan Tiriliyoyin da ake samu a ƙasar nan duk shekara.
‘Yan ta’adda na cigaba da kai hare-hare a arewa maso yammacin Nijeriya da tsakiyar Nijeriya a yankin arewa maso gabas inda suka kwashe sama da shekaru 13 ana tada ƙayar baya.
'Yan bindigar sun addabi al'ummomin yankin inda suke kai farmaki ƙauyuka, suna kashewa tare da yin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa tare da kona gidaje bayan sun yi awon gaba da su.
No comments