Daga Muhammad Awwal a Minna Ƙungiyar 'Arewa New Agenda (ANA)' ta shirya wani taron wayar da kai ga shugabannin ƙungiyoyin musulmi da...
Daga Muhammad Awwal a Minna
Ƙungiyar 'Arewa New Agenda (ANA)' ta shirya wani taron wayar da kai ga shugabannin ƙungiyoyin musulmi da Malaman addinin musulunci game da wa'adin da aka sanya na biyan kuɗin kujerar aikin Hajjin bana. Taron ya gudana ne garin Mina na jihar Neja cikin makon nan.
Shugaban Ƙungiyar na ƙasa, Sanata Ahmad Abubakar, ya bayyana cewa kashi saba'in da biyar cikin ɗari na kujerun aikin Hajji da 'yan Nijeriya ke zuwa daga yankin Arewa ne, wanda kuma har yanzu ba a biya kashi goma sha shida cikin ɗari na kujerun ba, ga shi ƙarshen watan nan ne wa'adin.
Ya ce, "Ganin yadda Hukumar ƙasar Saudiya ta ɓullo da sabon tsari, Ƙungiyar mu ta ga dacewar shirya taron gaggawa don faɗakar da Malamai da shugabannin Ƙungiyoyin addinin musulunci muhimmancin wayar da kan al'umma, musamman masu ƙudurin zuwa aikin Hajji a wannan shekarar."
Sanata Ahmad, ya ci gaba da cewa, kamar yadda gwamnatin tarayya ta yi hoɓɓasa ganin an samu daidaito, Hukumomin Saudiya sun tsaya kai da fata akan cewar duk Alhajin da ya kasa cika wa'adin biyan kuɗin kujerar nan da ƙarshen watan Disambar wannan shekarar, to ya tabbatar da ba zai samu damar aikin Hajjin bana ba.
Ya ƙara da cewa, wannan aikin na wayar da kai, ba na gwamnati kawai ba ne, ya zama wajibi duk wanda ya ji ya sanar. Ganin Malamai na bakin ƙoƙarinsu a wuraren ibadah, shugabannin Ƙungiyoyi na ƙoƙari a wuraren wa'azozi da lakcoci, shi ne su ma suka ga dacewar su sanar da su domin su sanar da al'umma.
Wannan sharaɗin ba na gwamnatin tarayya ko Hukumar Alhazai ba ne, sharaɗi ne da Hukumomin Saudiya suka fitar, saboda kimiyyar zamani ta zo koma, ana son ƙididdige shi kafin lokaci.
Ya ce, Hukumar ta baiwa Nijeriya kujeru dubu casa'in da biyar ne, amma har zuwa yanzu ba a samu adadin ko da kashi goma sha shida ba cikin ɗari na waɗanda suka biya kuɗin kujerar ba.
Shi kuwa Hon. Sani Mudi, wanda ya na ɗaya daga cikin jagororin Ƙungiyar, ya ce kungiyar su ta damu da ci gaban Arewa, matsaloli da ƙalubalen da ke gaban mu shi ganin saƙon ya isa wurin jama', domin ba maganar siyasa ba ce, sharaɗi ne da Hukumomin Saudiya suka gindaya, kuma mafi yawan masu zuwa aikin Hajji 'yan Arewa ne, "kuma rahoton da muka sam, har yanzu ba a samu kashi ashirin na waɗanda suka cika sharaɗin ba," in ji shi.
Ya ƙara da cewa, "Ba za mu jira gwamnati ba, domin lamari ne da ya shafi ɗaya daga cikin shika-shikan musulunci, wato sauke farali ga wanda ya samu dama. An samu sabon shugabanci a Hukumar Alhazan ta ƙasa, wanda mu ke kyautata zaton alheri gare ta."
Da yake ƙarin haske, Daraktan gudanarwa na Hukumar kula da jin daɗin Alhazai ta jihar Neja, Malam Attahiru Dukku, ya ce kuɗin kujerar bana Naira Miliyan Huɗu da Dubu Ɗari biyar ne, kuma ana biyan kuɗaɗen ne a asusun bank, tare da fasfo ɗin mutum, idan ka bada wani kaso cikin kuɗin, amma ka kasa cikawa har ranar talatin da ɗaya ga watan nan, babu na da biza, balle ka samu damar sauke farali.
Shi kuma Dr. Umar Faruk Abdallah, wanda shi ne Daraktan Hukumar kula da addinai ta jihar Neja, ya bayyana cewar hukumarsa za ta haɗ gwiwa da ma'aikatar kula da jin daɗin Alhazan ta yadda za a ƙarfafa gwiwar Malamai da shugabannin ƙungiyoyin addinin musulunci wajen ƙarfafa gwiwar faɗakar da al'umma kan wannan sabon tsarin da Hukumomin Saudiya suka fitar.
Ƙungiyar ANA ta shirya gaggawar ne bayan babban taron da Ƙungiyar Jama'atu Nasril Islam ta kira a Minna ta Neja, wanda mai Alfarmar Sarkin musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar ya jagoranta, tare da goyon bayan Sarakunan gargajiya kan ƙarfafa gwiwar al'ummar musulmi wajen haɗin kai da fuskantar matsalolin da ke tasowa a ƙasar nan.
No comments