Daga Muhammad Awwal, Mina Shugaban ƙungiyaf masu haya da babura ta Nijeriya, 'Motorcycles Operators Union of Nigeria (MOUN)', Kwamar...
Daga Muhammad Awwal, Mina
Shugaban ƙungiyaf masu haya da babura ta Nijeriya, 'Motorcycles Operators Union of Nigeria (MOUN)', Kwamared Julius Oghenevwegba Bobi, ya nuna matuƙar jin daɗi da yabo ga gwamnatin tarayya bisa rajistar da aka yi masu. Inda kuma ya yi alƙawarin bayar da cikakken goyon bayan su ga ga ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa.
Julius ya yi wannan yabo ne a lokacin wata tattaunawa da shugaban ma'aikatan ofishin Shugaban Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa NLC, yayin da suka je karɓar shaidar rajistar a ofishin NLC ɗin da ke Abuja a kwanakin bayan.
Shugaban masu haya da baburan ya ce, "Wannan wata babbar rana ce gare mu, wacce mu ka karɓi wannan shaida ta tabbatar da rajistar mu a matsayin ƙungiyar ƙwadago.
“Wannan ci gaba zai ba mu damar gudanar da ayyukan mu kamar yadda doka ta tanada, domin yanzu muna da izinin gudanar da ayyukan mu, ba tare da wata tsangwama daga kowace Æ™ungiya ba."
Daga nan sai Kwamared Julius Oghenevwegba Bobi ya ya ƙara miƙa godiyar su ga gwamnati, tare da ɗaukar alƙwarin gudanar da ayyukan su bisa doka da haɗin kai da sauran ƙungiyoyin ƙwadago.
No comments