Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Al'ummar Yankin Funtuwa Na Neman Agajin Gwamna Raɗɗa Wajen Ayyukan Raya Ƙasa - Rabe Mela Maska

Daga Imrana Abdullahi Alhaji Rabe Mela Maska, jigo ne a Ƙaramar Hukumar Funtuwa ta jihar Katsina, ya yi kira ga Gwamna Dakta Dikko Umar Raɗɗ...

Daga Imrana Abdullahi

Alhaji Rabe Mela Maska, jigo ne a Ƙaramar Hukumar Funtuwa ta jihar Katsina, ya yi kira ga Gwamna Dakta Dikko Umar Raɗɗa da ya taimaka masu da aikin hanyar da ta tashi daga Marabar Maska zuwa Maska, Tumɓurkai da sauran waɗansu garuruwa da dama a yankin.

Haka zalika Rabe Mela Maska ya kuma yi kira ga Gwamnatin jihar da ta gina masu Dam, wanda a can baya har an fara kawo kayan aiki irin su duwatsu da sauransu domin gina masu Dam tun daga Gadar Maska domin amfanin al'ummar ƙasa baki ɗaya.

Ya ce"Muna fatan Allah ya sa Gwamna Dikko Raɗɗa ya gama lafiya, Allah ya saka masa da alkairi, kuma bukatunsa na alkairi Allah ya biya masa, yadda sauran Gwamnoni suka yi shekaru Takwas suka gama lafiya, shi ma Allah ya taimake shi ya gama Mulkin sa lafiya. Domin haƙiƙa ya na taimaka wa talakawa ƙwari matuƙa, kuma muna jin daɗi fiye da kima."

Haka kuma Alhaji Rabe Mela Maska ya koka a kan wata hanyar da tsohon Gwamnan Jihar Katsina Barista Ibrahim Shehu Shema ya yi daga Marabar Maska zuwa Maska ta haɗa da waɗansu garuruwan da ake samar da amfanin Gona da yawa, inda ya ce wannan hanya ta lalace har ta kai ga zama tarkon mutuwa ga ɗimbin masu bin ta. 

Ya ce, hanya tun daga Tudun Iya, Maska zuwa Tandu, Tumburkai zuwa Ƙaura, Sabon Gida da Ɗantankari, duk a halin yanzu wannan hanya ta lalace, ba ta biyuwa cikin daɗin rai, duk da irin yadda ake fitowa da ɗimbin kayan amfanin Gona. 

Ya ci gaba da cewa, "Saboda haka ne muke yin kira ga Gwamnan Jihar Katsina da mu ma a taimaka mana kamar yadda ake ta bayar da ayyukan hanyoyi, mu ma a san da mu, a yi mana wannan hanya da na ambaci garuruwan da ta ratsa domin a gyara mana mu san a cikin Jihar mu ke. 

"Sai kuma na biyu, ga mu da gada, an kawo kayan aiki tun wajen shekaru Goma an yi dakin Dam, amma har dakin ya lalace. Amma tun da a yanzu lokaci ne na Noman rani, idan an datse Dam ɗin a duk yankin nan, ko daga ina lamarin zai ta fi daidai, a yi ta Noman rani a kodayaushe.

"Misali, idan mutum ya yi tafiyar kilomita Ashirin Gabas da Yamma, Kudu da Arewa, duk za ka ga ba Dam ga kuma ɗimbin manoma ta ko'ina, kuma a shirye suke su yi Noman rani, amma ba Dam.

"Saboda haka ne mu ke yin kira ga mai girma Gwamna da ya taimaka ya sa a yi mana wannan Dam domin a samu yin Noman rani, tun da duk ga Gonaki nan ba iyaka ta ko'ina a shimfiɗe."

 

No comments