Kotun Ƙoli ta amince da buƙatar Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da ke ƙalubalantar hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara na soke tuhume-tuhumen da ake yi ...
Kotun Ƙoli ta amince da buƙatar Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da ke ƙalubalantar hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara na soke tuhume-tuhumen da ake yi wa Nnamdi Kanu, jagoran ƙungiyar IPOB.
Kotun Ƙolin ta ce, dole ne Kanu ya fuskanci shari'a.
A watan Oktoban bara ne, wata kotun ɗaukaka ƙara ta bayar da umarnin a saki Kanu inda ta ce akwai kura-kurai a shari'ar.
Sai dai gwamnati ta sake shigar da ƙara inda ta ce Kanu barazana ne ga tsaron Nijeriya.
No comments