Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnonin Arewa Sun tallafa Wa Al'ummar Tudun Biri Da Naira Miliyan 180

  A wani taro da ta gudanar yau a gidan gwamnatin jihar Kaduna, Ƙungiyar Gwamnonin jihohin Arewa ta tallafa wa al'ummar ƙauyen Tudun Bir...

 

A wani taro da ta gudanar yau a gidan gwamnatin jihar Kaduna, Ƙungiyar Gwamnonin jihohin Arewa ta tallafa wa al'ummar ƙauyen Tudun Biri da tsabar kuɗi Naira Miliyan Ɗari da Tamanin ta hannun gwamnatin jihar Kaduna.

Shugaban Ƙungiyar, Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Inuwa Yahaya ne ya karanto sakamakon taron, inda Gwamnatin sun nuna alhininsu game da wannan mummunan ahu da ya faru. 

Daga Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa Gwamnonin na Arewa sun haɗe kan su don lalubo dawwamammiyar hanya ta magance matsalar tsaron da ya addabi yankin. 

Ya kuma bayyana cewa za su yo ƙoƙari wajen haɗa kan al'mmmar yankin wajen ganin samun daidaito da fahimtar juna a tsakanin al'ummar yankin. 

Gwamna Yahaya ya kuma bayyana cewa sun karɓi rahoto daga Shugaban kamfanin NNDC, inda suka ji matsalolin kamfanin, domin duba hanyoyin da za inganta kamfanin.

Wakilin Matattarar Labarai da ke zauren da aka gudanar da wannan taro, ya shaida  mana cewa ya tsinkayi Gwamnonin Zamfar, Dauda Lawal, na Borno, Babagana Zulum, na Katsina, Dr. Dikko Umar Raɗɗa, mai masaukin Baƙi, Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani da kuma Shugaban Ƙungiyar, Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe. 

Sannan kuma sauran jihohin sun samu wakilcin mataimakan su. 

No comments