Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sarkin Sudan Ya Hana Hawa Idi Saɓanin Sanarawar Sarkin Musulmi

Daga Muhammad Awwal  a Minna A zaman fada na ranar Asabar 16th Disamba, 2023, Mai Martaba Sarkin Sudan Kontagora, Alhaji Muhammadu Barau Mu...

Daga Muhammad Awwal  a Minna

A zaman fada na ranar Asabar 16th Disamba, 2023, Mai Martaba Sarkin Sudan Kontagora, Alhaji Muhammadu Barau Mu'azu II, tare da 'yan majalisar sa sun ɗauki matsaya ɗaya kan Tungan Sani, ƙarƙashin Kulho a Karamar Hukumar Mashegu da ma sauran garuruwan da ke ƙarƙashin masarautar Kontagora kan ƙin yin sallar Idi a ranar da Mai martaba Sarkin Sudan ya hau, wanda kama Sarkin Musulmi ya sanar.

Wannan hukuncin ya biyo bayan ƙarar da aka kawo masa ne na Malam Abdullahi, shugaban wata ƙungiya da ke iƙirarin 'YAN SAISUNGANI ko 'ƳAN SALAWUDDIN da ya bijire wa wasu ƙa'idojin da suka saɓa wa masarauta da addinin Muslunci.

Mai Martaba Sarkin Sudan ya zartar da hukuncin ne gaban jami'an tsaro, ciki har da na fararen kaya. Sannan ya ce masarauta za ta ci gaba da bibiyar dukkan lamurran su don ganin ba su saɓa wa hukuncin da masarauta ta ɗauka akan su ba.

A ƙarshe mai Martaba Sarkin Sudan ya umurci shi shugaban nasu, Malam Abdullahi da ya kawo mashi shaidar takardar sa ta zama ɗan ƙasa, domin bayanai sun zo ma masarauta cewar shi Malam Abdullahi ba ɗan ƙasa ba ne.

Wakilin Matattarar Labarai ya binciko mana cewa, Masarautar Kontagora na yaƙi da rashin gaskiya da tabbatar da adalci, tare da maganin duk masu bijire wa umurnin shugabanni, matuƙar suna kan gaskiya.


 

No comments