Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Wa'adin Biyan Kuɗin Hajji; An Yi Kira Ga Maniyyata Su Gaggauta Biya, Lokaci Na Ƙurewa

Daga Muhammad Awwal a Minna  An yi kira ga al'ummar musulmi, musamman masu ƙudurin zuwa aikin hajjin bana da su gaggauta biyan kuɗaɗen s...

Daga Muhammad Awwal a Minna 

An yi kira ga al'ummar musulmi, musamman masu ƙudurin zuwa aikin hajjin bana da su gaggauta biyan kuɗaɗen su idan suna da hali, bisa la'akari da cewa lokacin da Saudiyya ta zayyana don rufe biyan kuɗin ya na ƙaratowa, wato ƙarshen wannan wata na Disamba.

Babban Limamin masallacin Juma'a na Tunga da ke Minna, Sheikh Barista Salisu Maidala'ilu ne ya yi kiran lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala sallar Juma'ar makon nan a harabar masallacin.

Shehin Malamin, ya ci gaba da cewa, "daman Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa, ya ce 'ku yi aikin Hajji tun kafin a hana ku. Wannan salon na bana da hukumomim Saudiyya suka ɓullo da shi da sunan zamani, salo ne na ganin nan gaba sun hana al'ummar musulmi sauke ɗaya daga cikin farillan addinin su, wanda kuma yana ɗaya daga cikin makircin Yahudawan da Saudiyya ta ba su daman kutsawa inda ba su da hurumin yin hakan."

Malamin ya ci gaba da cewa, "Tun da Yahudawa suka samu damar kutsawa a hurumin da ba na su ba, lallai sai al'ummar musulmi sun ga baƙin abubuwan da suka saɓa wa addini daga hukumomin Saudiyya.

"Tunda abin ya zama haka, kar mu yi fushi, duk yanayin da za mu samu kan mu, mu tabbatar mun sauke wannan nauyin idan muna da halin hakan.

"Mun sani da sauran lokaci, amma tun da yanayin ya zo da hakan, ina kira ga Malamai da sauran shugabannin ƙungiyoyin addini da su ƙara ƙaimi wajen faɗakar da masu hali kuma masu ƙudurin zuwa aikin Hajjin na bana da su tabbatar sun cike wannan wa'adin da samun ziyarar aikin Ibadah kafin lokacin da za a hana su saukewa.


No comments