Jami’in Hukumar Tsaro ta NSCDC, Shem Obafiaye, wanda ya shahara da kalaman ‘Oga At The Top’, ya samu ƙarin girma zuwa muƙamin mataimakin Kwa...
Jami’in Hukumar Tsaro ta NSCDC, Shem Obafiaye, wanda ya shahara da kalaman ‘Oga At The Top’, ya samu ƙarin girma zuwa muƙamin mataimakin Kwamanda Janar (CG).
An bayyana ƙarin girman ne a ranar Juma’a a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na hukumar NSCDC, Babawale Afolabi.
A shekarar 2013, Obafiaye, wanda shi ne Kwamandan Hukumar NSCDC a Legas, ya samu karɓuwa sosai a lokacin da yake fitowa a shirin karin kumallo na gidan talabijin ɗin, Sunrise Daily.
Lokacin da aka nemi ya samar da manhajar yanar gizo na hukumar NSCDC a Legas, Obafaiye ya amsa da cewa, “Shafin yanar gizon nan bai samu ba… sai dai a yi haƙuri… a jira… Oga na a sama ne kawai zai iya samar da shi,” yana nuna sama yana murmushi.
Kalmar “Oga At The Top” ta yi saurin yaɗuwa, ta rikiɗe zuwa barkwanci, waƙoƙin rawa, har ma ana buga su akan T-shirts da ke nuna alamar Obafiaye.
No comments